Sunday, 30 October 2016

Kursum 66 to 70

[25/09 8:10 pm] Xarah bukar✍🏻✍🏻:💞
*Kursum*
           
           By ~ Xarah Bukar

6⃣6⃣✨

hankali tashe umma tace son karka ce haka, gobe daurin aure atleast ka bata chance, " rai abace yace I'd rather die than 2 marry her, auran ne nafasa "ido jajir kursum tace yaya nasan u are angry, ko mi kamin I deserve it but plz karka rabani da hanifa, ita kadai na mallaka a rayuwata, ya wurga mata harara, baki da wata rayuwa data wuce ta prison, so keda hanifa har abada, "salma da inna dake gefe duk jikin su yay sanyi, abu  da suke tsoro yafaru.....huzaifa yace calm down bro, kabari  ayi komai cikin hankali, kar kayi abunda zaka zo kana regretting....Abba  ya daka masu tsawa, banason xancen banza, officer kuyi abunda ya kowa ku, kubarmin gida, ba shiri suka sa kursum a mota suka wuce station, kanwar abba  antee saude ta kwashe da dariya, Allah ya kara, ga namu ya'yan aka tsallake su, aka fita waje naima na titi, tunda anfasa auran bari mu tattara mu koma inda muka fito....Abba yace babu inda zaku, ya kalli umma, duk laifin kine, koda yaje  yayi auran sa na farko banda labari sai daga baya kika gaya min, dan kunga Ina shiru shiyasa kuke min abunda kukeso, toh baku isa ba aure dole a daura game rabo, dan baza a mai dani karamin mutum ba," lokaci guda umma da ya yazid sukace dawa zaa daura ???, yace idan an daura gobe kwaji, na gama magana....fuuu ya wuce ciki afusace....shima ya yazid ya wuce daki rai abace, sai yanxu yasan zafin da ake ji idan aka yaudari mutum, "huzaifa ya kira salma su wuce, dan zamansu ba amfani....." Meerah tace galfrnd let go, kinsan yau akwai celebration, zee ta murmusa, ki bari zuwa gobe, am very sure dani xaa dauran auran, suka kwashe da dariya suka bar gidan.

Gidan tsit, kaman ana zaman makoki, gaba daya hankalin umma ya tashi, ya zama dole ta gayawa hajiya kursum na raye, dan ita kadai ce zata iya taimakon ta, da sauri ta dauki mukullan mota ta fice.

        *Police station*

Hey pretty gal ki mana shuru, kinyi laifi an cafko ki kin ishemu da kuka, "ta balla mata harara, ina ruwanki dani....police woman ta gyara tsayuwa, tace kin  shigo hannu, so karki kuskura kice zaki min fitsara, ta wurga mata kayan dake leda,na baki 10mins ki cire na jikinki kisa su...

Umma ce zaune a office din d.p.o suna xantawa, tace ka taimaka ko nawane zan bada ayi realising dinta on bail, banason tayi kwanan cell, d.p.o yayi gyaran murya, gaskia hajiya her case is critical, yanxu an mata transfer to federal prison, dole sai an shiga kotu, shawarata shine Ku sama mata lawyer, idan kuma babu akwai lauyoyin gwamnati, suna iya tsaya mata, umma ta nisa, toh shi kenan zamu samo lawyer, amma da wuri mukeso ashiga kotu, "d.p.o yace indai akwai lawyer ba matsala, yau Friday zuwa next week ana iya shiga kotu, tace toh, xan iya ganinta ??  yace kwarai kuwa, ya kira sergeant, maza kaita cell 0644, sergeant yace ba kowa, duk suna mota xaa wuce dasu prison, d.p.o yace ok rakata waje, kafin su wuce, da sauri ta mike suka fice

Prisoners ne wajan talatin sanye da blue riga da wando cotton, sunyi layi suna shiga katoton luxurious bus mai tambarin federal prison ajiki, ga yansanda ta ko ina a tsatsaye, sergeant ya kwallawa madam kofo kira (police woman dinnan), ta karaso tana cika tana batsewa, "oga yace akawo hajiya taga prisoner din da aka kawo dazu, " madam ta karewa umma kallo tace tana cikin mota already, saiko ta window zaki mata magana na minti biyu kacal, umma tace hakan ma nagode muje, suna tafe umma tace madam officer nasan kune in charge of tsare prison din,  taimako nakeso gareni, "wani iri kenan?? inaso ki kulanmin da yarinyan nan, banaso ta wahala a prison, ko nawa kikeso xan baki, " madam ta washe baki, karamin aiki kenan, indai zaki bani dubu dari biyar cash, toh babu wanda zai taba ta, "umma tace nakara miki #200k asama, ta fiddo card dinta, gashi ki kirani, ki turo min account details dinki, zakiji alert as soon as possible, " madam tace angama hajiya, suka iso bakin motan tace ga yar'ki can last window, minti biyu na cika xanja mota....."tana zaune tayi tagumi, banda sharar kwalla da take, kursum!!! taji muryan umma na kiranta, da sauri ta juya taganta tsaye side window, tayi nairai da ido, umma kiyi hakuri ki yafeni, Allah yaga zuciya ban cuce kowa....."shtss karki kara ban hakuri inji umma, nasan baki da laifi, duk abunda ya samu bawa Haka Allah ya kaddaro, shiyasa nakeso ki kwantar da hankalin ki, ina nan tare dake, "ta fashe da kuka, umma ina hanifa?? tana gida wajen inna, karki damu nace ta kula da ita....zata kara magana mota ta tashi, da Sauri tace umma ki cewa mamata ina gaishe ta....toh kawai umma tace a sanyaye, suka ja mota suka wuce....

Tsinan niya dama nasan da wani hidden agenda kika zo gidan nan,"ta kalle shi a wahalar ce, dakyar ta iya cewa shehu sake min wuya karka kashe ni, ya kara sheke wuyan dakyau yace kinsan cewa kursum ba sumy bace shine kika boye mana koh ? "gimbiya tayi tsuru da ido, bangane ba...yace munafuka ai bazaki gane ba,  indai kinason zaman gidan nan dole kije kotu kiyi testifying karya akan ta, nafiso ta dauwama a prison, idan kunne yaji jiki ya tsira, yayi wurgi da ita kan gado, ya fice afusace, " da sauri ta mike tsaye tana maida numfashi, ta karasa gaba mirror tana kallon yadda wuyanta yayi jajir tsabar damka, aranta tace ohh su kursum asiri ya tonu kenan, lailai ko dole tayi magani baba shehu, dan ta lura shima kwadayin arzikin yake, ta fito tana zake zaken azuci, xata sauka kasa taga umma ta shigo gidan, da sauri ta koma, ganin umma ta shiga dakin hajiya itama taje ta labe bakin kofan....."hajiya dake kwace ta yunkuro dakyar ta zauna akideme tace kina nufin kursum ya'ta ce ?? kwarai kuwa itace bata mutu ba, ke kadai ce zaki iya kubutar da ita daga prison, hajiya ta sauke doguwar ajiyar zuciya tace nayi losing dinta d first tym, diz tym bazan bari ta kufce min ba, I have to save her, da sauri tadau waya ta kira barrister shu'aibu, "cikin minti 10 ya iso gidan, gimbiya dake labe tabar gun da sauri ta koma daki a kideme, idan kursum tabar prison kashin su ya bushe, dole tadau mataki...

Barrister shu'aibu yace hajiya kwantar da hankalinki, wannan case din mai sauki ne, u'r her mom ke dayace zaki iya kubutar da ita daga zargin fraud da ake mata tunda she is d legal owner of d company, indai kikai testifying a court angama," umma tace kasan harda identity theft, ya kenan ? yace inde xaa samu wanda xai bada good testimony akan relationship dinta da marigayiya toh she is save.....hajiya ta nisa tace ba matsala, gimbiya xatai testifying tunda tasan dey are best friends, yace toh shikenan, xanyi kokari zuwa Monday ashiga court, yamasu sallama ya fice, umma ma tamike yamma tayi zata wuce....

*Federal Prison*

Babban prison mai dauke da 6 story building, kowa sanye da blue uniform, wasu na field suna playing basketball, daga gefe kuma wasu ganda ganda mata ke  busa sigari suna caca.......new inmate da aka kawo sunbi layi ana nuna masu cell dinsu, "ana zuwa kanta madam kofo tace pretty gal ur cell is over dia, come wit me...atsorace kursum tabita abaya, danta lura da irin kallon da prisoners din ke mata...tayi pressing lock, cell din ya bude, tace ga naki, if u need anytn kimin magana, "kursum ta karewa cell din kallo, duk yafi sauran kyau da girma, gashi so comfortable, fully-furnished tare da A.c, television da fridge, ta juyo ta kalli madam, nagode sosai, tace don't thank me, ki godewa mamanki itace ta biyani in kula dake, " kursum tayi shuru tabbas tasan umma ce, Allah ya saka mata...."madam ta kira wata tsohuwar prisoner mai suna Lady D, daga nin  ta kaga rikakkun mata masu duniya, gabadaya jikinta zanan tattoo ne , fuskan nan babu annuri, ga wasu prisoners uku na taka mata baya, "madam tace lady nabaki in charge of safety din yarinyan nan, ko kwarzano ban yadda amata ba, lady 
ta kalli kursum up & down tace expensive property koh ?? Kofo tace datx none of ur bizness, ki kulun min da ita kawai, "tace okay no p....

Kwance yake kan bed yayi ruf da ciki, gaba daya duniyar tamai zafi, kuka kawai yake hankali tashe, ya azabura ya mike yahau wurgi da pillows tare da naushin walls din dakin, afili yace " y my witch, y did u betray me, kece rayuwata, d only gal I can die for.....yakara fashewa da kuka mai tsuma zuciya....umma dake tsaye bakin door ta karaso ciki da sauri ta rike hannun shi dake zubda jini, "agigice tace my son plz don't hurt urself, kayi hakuri ka yadda da kaddara, komi yafaru is already written, ya dago idonsa daya canxa launi zuwa ja yace umma am shattered, d only gal I loved broke my heart, " kar kace haka son, nasan she loves u alot, kodan darajan hanifa yakamata ka yafe mata, gashi kuma abbanka yace zai aura maka wata, ya zamuyi kenan ??? yace I don't care, kowa abba ya daura min I will accept cox my daughter need a mother, "ta kalle shi da mamaki, tace u don't care fah kace ? yace yes.....tace okay, ta fice afusace......ta iske abba a daki yana danna lapton, ta zauna a sanyaye tace Alhaji, " ko dagowa bai ba yace ina  jinki....,dan Allah dawa zaka daura mai aure gobe ? "Fuska amurtuke yace da zainab diyar shehu xaa daura, dama itace zabina tun farko....ta dafe kirji, alhaji kar kayi haka, yarinyan nan sam bata da kunya, ka taimaka ayi auran da kursum, itace zabin shi...." ya kara bata rai, tunda kinyi insisting, na yadda toh, zan aura masa zabina da zabinki, agigice tace su biyu zai aure ?? "yace eh amma on one condition, karki kara shiga lamarin Kursum na yanke alakar dake tsakanin ku, infact ko court kika je ko prison ganinta abakin auranki...........😳😳

*Xarah Abubakar*😘
*Dedicated to Badia*

~luv u ol~😘

[04/10 6:12 AM] 💕: [28/09 12:49 pm] Xarah bukar✍🏻✍🏻: 💞
*KURSUM*

           By ~ Xarah Bukar

6⃣7⃣✨

Washe gari

An shaida daurin auren su
akan sadaqi 100k nako wacce, baba shehu sai yaken dole yake, yaso ace abba ya hakura da batun Kursum, amma sai yazo mai da xancen hadasu auran da zee, ba yadda ya iya shiyasa ya nuna hakan ma daidai ne...jiki a sabule ya dawo gida, meerah da zee dake zaune a palo suna jiran good news suka   tsorata ganin ya shigo fuska amurtuke, "zee tace baba lafiya dai koh ?? ko badani aka daura ba....ya nisa yace zainab sai dai kiyi hakuri,  ku biyun aka daura masa, wat ta kwalalo ido diz cnt b possible, shifa ya yazid da bakin sa yace bazai aureta ba, hw cms ya canxa mind...baba shehu yace I don't tink yazid yasani, danko daurin auren baije ba, it seems iyayen kawai suka san xancen, zee taja tsaki, am very sure uwarsa ta hada komai shegiar mata, aiko xanyi maganin ta...."indai kinason zaman lapia kuma danta ya soki dole ki girmamata, cox idan aka sakoki babu ruwana, namiki iya kokari na, ya haura sama abunshi

Meerah tace calm down, auren bashi da amfani ai, tunda Kursum din na prison, " idan tafi to fah ya kenan ?? ta kwashe da dariya, ai bazamu bari ta fito ba, zee tace bangane ba ?? meera tace ina da connection a prison din, kudi kawai zamu biya agama da ita, atsorace zee tace akasheta kenan ? kwarai kuwa, idan ta mutu kowa ya huta, zee tace idea  din yayi amma it risky, bari musan yadda trial dinta zai kasance tukun, meerah tace toh let wait n c, yanxu muje ki kwashe kayanki, xan kira frnds dinmu suzo mu rakaki gidan miji dan banga alama abokan ango zasu zo ba, zee tayi dariya, wlh kaman kin sani, muje ki tayani hada kaya🏃🏃�🏃�

Kusan sau uku yana knocking kofan ba respond, ya murda yaji gam kofar a kulle, ya leke dakin gimbiya, ke hafsatu ina hajiya ? kota fita ne ? naga kofar ta rufe, gimbiya dake shafa mai ta juyo ayatseni tace hajiya bata nan, tun safe ta tafi zamfara ganin mai magani ciwon baya ita da samira, yace miyasa bata gayamin ba ? tace oho nasani, tacemin in gaya ma zata dade, ba saika naime taba, idan tayi settling zata kira ka....toh kawai yace, sam bai damu ba, dan zaman hajiya agidan bashi da amfani.

Prison

Yau sanitation tun safe suke gyare gyare, lady D na hakince kan kujera tana basu order, "kursum na daga gefe tayi tagumi, duniyar ta mata zafi, bata taba expecting ya yazid zai guje taba, gashi wani irin so da kaunar shi ke ruruwa cikin zuciyar ta, " dukan da taji abayanta yasata dawo hayyacinta, a tsorace ta dago, Ta kare mata kallo, irin matan nan ne masu kirar maza, fuska bakikirin ba annuri, da kyar tace baiwar Allah lapia kika dakyan ?? Matar da ake kira da snake ta balla mata harara, koma waye ubanki we are all criminals anan, banga dalilin da zaisa muna aiki ke kina zaune kina kallon mu baaa...tasss kakkaywan mari da taji afuska ya hanata karasa wa, "rai abace lady tace how dare you touch my property...." tsum snake tayi, shikenan kashin ta ya bushe, baki na rawa tace lady am sorry bansani ba, lady ta kara wanke ta da mari, ba shiri ta duka kasa tana bada hakuri, lady tace next tym kika tabata am gonna cut off ur hands, ta kalli kursum, hop u are okay ??  akidime tace yes, dan ba karamin tsorata taiba akan cire hannu da xaai...."madam ta karaso wajan tace meke faruwa ne ? da sauri snake tace notin, we are just talking, tasan halin madam sarai tana iya kaifa solitary for 2weeks, madam tace okay, ta kalli kursum, maza kije waiting room, sm1 is dia to c yhu, "tace toh, da sauri tabar gun da murnan ta, tana patan Allah sa ya yazid ne yaxo, " tana shiga taga barrister shu'aibu, suna gaisa tana binsa da kallon mamaki, yace kar kiyi mamaki, nine lawyer  mai kareki....."uhmm daka barni kawai, nida banda ko sisi biyanka..
      " yay murmushi, karki damu, yanxu gayamin dangartakar ku da sumy ? "ta nisa sannan tamai bayanin komai, yace toh shikenan, don't bother urself, idan mun shiga court  gimbiya da hajiya are d perfect witness to diz case, " tamai kallon rashin fahimta, tace bangane ba, hajiya da bata kaunar ganina, how cms zatai testifying, mi zata ce ??
      "yace i cnt say, amma kisani duk abunda zata ce shine zai ceceki, " tayi shiru, itadai tasan babu wani good relationship tsakanin ta da ita, Allah kadai yasan abunda zatace, tace nagode sosai brstr, "yace karki godemin, hajiya zaki godewa, ya mike tsaya, ni xan wuce sai mun hadu a court, sukai sallama ya fice.....itama ta koma ciki a sanyaye..

Gidan shiru kaman ba buki ake ba, gaba daya yan'uwa sun tattara sun tafi, umma da abba ne kadai zaune a Palo suna hira kasa kasa, "yace kin nace ayi auran gashi anyi, miye kuma bakyaso yasani, " kyale ni dashi kawai, so nake na nuna mai kuskuran sa, tunda ka zaba mai zee amatsayi mata ai shi kenan, "ya gyara hulan shi yace Allah ya kyauta, ya mike ya fice..
       " yazid ya shigo fuska amurtuke ya zauna, umma ina wuni ??
     "ta amsa lapia, fuska daure
      " yace yanxu umma abunda abba yayi ya dace, ya xaai ya daurin min daure da zee, dat gal is crazy, "umma ta balla mai harara, I tot kace kana iya auran kowa ya zaba ma, miye kuma kake complain, kaje ka zauna da zee tunda ita abba keso..." Xai kara magana tayi saurin taran numfashin sa, ya isheni haka, kamin shiru kawai
        "yay shiru, yarasa laifin da yayi umma ke fushi dashi, daga bisani ya mike yaje daki ya zaune..

Ganin yammata kusan su hudu na  shigo da akwatuna, yasa ta mike tsaye ta kare masu kallo, tace Ku kuma daga ina babu ko sallama zaku shigo min gida har cikin Palo ?? daya daga cikin su tace amarya muka kawo..."umma tace lailai kam wace marar kunya amarya ce  daku zaku kawota?? "Ni CE nan, ta shigo tana rangwada, meerah tace umma munzo siyan baki, ina  mijin yake ne ?
     " haushi da takaici ya hana umma cewa uffan, tadau wayanta ta shige daki...
     zee tace woww, Ku zauna plz feel at home, barin kawo mana drinks, suka zazzauna suna shewa, ta dauko tabasu, suka baje suna hirarsu ta batsa, ba kunya ba tsoron Allah, meerah tace galfrnd ina yake bangan shiba,tace I tink yana daki, barin je insa meshi, "eh kije, kinsan lallaba shi zakiyi har ya tsaki jiki, tace toh, da sauri taja akwati ta wuce dakin shi....

Yana zaune ya kafawa waya ido, ahankali nima na leka, ba komai yake kalla ba face picture dinta daya daura a screen saver, ta turo kofa ta shigo, ya dago sukai  4eyes, " rai abace yace ke kuma fah ,miye na shigo min daki harda tarkace ?? "ta karaso gabanshi tace haba baby am now ur wife, kuma kasan gatan mace dakin mijin ta, " yay banza da ita... my love say sumtn mana, kayi shuru....ta matso dab dashi zata shafa mai fuska, da sauri ya mike akufule, karki kuskura ki tabani, just stay away from me...fuuuu ya fice, "taja uban tsaki, ta dau wayansa taga ashe pic din Kursum yasawa ido, lailai har yanxu yana sonta kenan, aiko zata dau mataki  tun kafin ma yasan an aura masa ita...

Wani kololon bakin ciki yaji ganin su a Palo sai hauka suke, "ya daka masu tsawa, ba shiri suka kintsu, yace koku bar gidan nan ko yanxu yan'sanda suzo su tafi daku, caraf meerah tace haba yaya mi yayi zafi haka, we are just leaving, ta kalli sauran let go, suka mike tsum tsum suka fice, " yaja  tsaki yace wace irin rayuwa ce wanan (🙄 idan ka tambayeni in tambayi wa😕) yadau mokullin mota ya fice daga gidan......"ta sauko tana cika tana batsewa, taga ba kowa Palo tace badai sun tafi ba, ta leka kitchen taga inna zaune da hanifa tana bata abinci, taja tsaki, ta karasa ta dauke hanifa, ke tsohuwa nice uwar hanifa yanxu, so ki tattara ki koma kauyen da kika fito, "inna tace yarinya ba saikin zageni ba, zan tafi, amma kiji tsoron Allah idan kika zalinci hanifa zaki hadu da hukuncin ubangiji, " zee tace naji, ki tafi kawai mun hutar sheki, "barin shiga enma umma sallama, " ta wurga mata harara, babu inda zaki, daga nan gate zaki wuce straight, "toh kawai inna tace tadau gyalanta tabar gidan....

Bayan kwan  biu

Federal high court⚖
11.45am
 
Duk sun hallara ana jiran  karaso wan alkali, ko wanne su da mugun abunda yake ainawa cikin zuciya sa, banda salma da huzaifa da sukai shiru suna jira suga kursum, salma tace yaya kana ganin xaa dace kuwa, yanda nake ganin su baba shehu ko ajikin su, "yace kalesu, ta Allah ba tasu ba...." meerah dake Zaune ta baya, ta tabo zee tace babe hw far na, ya yazid baze zoba ?? "I don't tink zai zo, nifa ko magana bayamin, ya hanani zuwa kusa dashi, " kai haba dai, kice ko first nyt baku yiba, "uhmm shida ko kallo na baiyi balle ma ayi harka, idan nayi kokarin cusa kaina tashi yake yabar min bed din, ita kuma umma bana ma ganinta, she is alwayz indoors, meerah tace gaskia baya da mutunci, zamuyi maganin shi..
         " Gaskia munyi dabara fah, yanxu dai zamuga waxai ceceta, gimbiya ta murmusa, kedai bari, ai suda ganin hajiya har abada, saidai Kursum ta fada duniya, babu mai tallafa mata, "hinde tace aiko dai, naga shehu sai fara'a yake..." kyaleni dashi, nariga nayi planing abunda zan mai, bari agama da yarinyan nan tukun..

Barrister shu'aibu ne zaune, ya duba tym, yay tsaki, yakamata ace hajiya ta zo, ga line dinta switch off, da sauri ya fita wuje ya kira layin umma, tana gani ta dauka da sauri...
         "Hello barrister har kun gama ne, " yace yanxu dai xaa fara, hajiya shuru bata zoba...
    "tace haba dai, kodai mantawa tayi, barin tura huzaifa yanxu nan yaje ya dauko ta, ta kaste
    kusan minti biyu huzaifa ya fito da hanzari shi, brstr yace karka dade plz, ita kawai muke jira, " yace yanxu kuwa, yaja mota da sauri ya wuce..

yana komawa ciki, alkali harya shigo ya zauna, yan'sanda suka shigo da Kursum, duk suka bita da ido, zee taja tsaki, tana prison amma she still  looks good..🙄

Alkali ya kalli papers dake gabanshi sannan ya dago yace the defendant is accused of  I.d, fraud & kidnapping and plead innocence, "prosecutor yace haka ne, ina so court taban dama in mata tambayoyi, alkali yace an baka, " ya karaso gaban ta yace muna iya sanin cikakken sunanki, ta fada agajarce, dan tsayuwar ta fara isarta, yace miye hujjarki na kidnapping yarinya bayan kinsa itace ya kamata ta gaji makudan dukiyar da kakanta yabari amma ke kika gaje alhalin baki hada komai da ita da, caraf brrst shu'aibu yace objectn my Lord, tambayoyin nan basu dace da shariar nan ba, alkali yace objectn sustain, kidnapping  case  is dismissed tunda actual family din basuyi pressing charges ba, prosecutor yace toh inaso Alhaji shehu fito ya bada  sheda akan yadda tayi running company din 4 almost a year, "baba ya Mike da sauri ya karasa witness stand, prosecutor yace ya lamarin company ya kasance tun lokacin da ta maye gurbin shugaba ??
    " ya nisa, gaskia tunda tazo komai ya tsaya cak, ga makudan kudade an naima an rasa, kusan wata hudu baa biya workers ba, prosecutor ya kalleta, ina kika boye kudaden da aka rasa, ko kina da foreign account inda kike tarasu ??? tayi tsuro da ido, aranta tana mamakin karya irin na baba shehu, dakyar tace ban boye komai ba, kuma bani da labarin missing kudade, "ya kalli alkali yace nagama tambayoyi na, brrst shu'aibu ya mike tsaye, ko hajiya hafsatu zata iya fitowa, tsum gimbiya ta mike, tazo stand, yace munsan ke kika rainasu tun suna yara, kina iya bamu kataican can tahiri akan dangartakar wace ake tuhuma da marigayiya ?? " kwarai kuwa nice amatsayin uwarsu basu da kowa agarin saini, tun asali Kursum bata da aminiya data wuce sumy, kowa yasan su tare, amma dayake Kursum akwai hassada da kwadayin abun duniya, shiyasa sumy ta rabu da ita, dan randa zasu tayi kano har office sumy tazo tasami tace koda ta mutu Kursum CE ta kashe ta, dan tana yawan threatening dinta akan idan bata bari taje gidan su ba......daga brrst har kursum tsakin baki sukai jin makircin da gimbiya ke kullawa, brrst yace waye shaden ki lokacin da tazo office dinki ta gayamaki ??? "tayi shiru, prosecutor yay objecting, alkali yaba shi dama, " ya karaso gaban gimbiya, yace kinsan cewa wace ake tuhuma ta saci rayuwar mai rasuwa, miyasa kikai shuru baki gayawa kowa ba, kenan kema u are her accomplice, "gimbiya tace cemin tayi zata kasheni idan na tona, shiyasa nayi shuru da bakina, " yace toh, kina iya komawa ki zauna..

Duk ya kideme banda zufa ba abunda yake, bai yi tunanin haka case din xaiyi zafi ba, ga har yanxu hajiya basu zo ba, ya kalli alkali, inaso court taban minti goma kacal har main witnesses din  ta karaso, "alkali yace baa haka a court, every1 is expected to be here, tun kafin in shigo, amma nabaku minti 5 kacal....

Kusan minti biu shuru, babu ma alaman su, gashi ba daman making call, gimbiya sai fadada murmushin ta take, minti biyar na cika, alkali ya buga tambari yace since d defense witnesses is not here to testify, d defendant is declared guilty......😳😳

*Xarah Abubakar*
*Dedicated to Badia sallau*😜

~luv u ol~😘😘
[04/10 6:12 AM] 💕: *KURSUM*

          By ~ Xarah Bukar

6⃣8⃣✨

Kana nufyn ba kowa agidan ?? "mai gadi yace tabbas ba kowa, da zasu fita sukace arufy ko eena
       " hajiya bata ciki ne ?? yace eh bata nan, alhaji shehu yacemin tayi tafiya kwanaki biu da suka wuce, "okay tau nagode, ya koma mota, ya fiddo waya yay dialing no din umma, bugu daya ta dauka..
    " huzaifa ya ake ciki ? kasa mae ta?
      "ya nisa yace umma akwai matsala, hajiya bata gari, sunce  tayi tafia..."tayi shiru, daga bisani tace toh shikenan ka koma court, xan cigaba da trying line dinta, yace okay, sukya sallama...
      " jiki asanyaye ta ejiye wayan, tana mamakin ina hajiya taje alhalin tasan yau ne trial din, gaskia sumtn is fishy ba yadda xaai ace bata nan, amma zata bincika dai..

Court

Duk sun girgiza da kalaman alkali, banda mutane hudu da suka kara fada'da fara'ar su, "alkali ya cigaba da magana, due to rashin hujjoji masu karfi, wace ake tuhuma ya zama dole tayi zaman kurkuku na wata uku...." dumm gaban kursum ya fadi, dagowa tayi ta karewa gimbiya da baba shehu kallo mai dauke da tsana, tasan sarai sune suka ja mata kuma ta tabbata harda hadin bakin hajiya, brrst shu'aibu ya karaso wajanta yace kwantar da hankalinki, nasan uxuri ya hana hajiya xuwa, muna da daman kara bude case din anytym, idan har taxo tayi testifying u are save, "ta kalle shi da idanuwa ta dasuka sauya launi zuwa ja tace indai hajiya ce xata taimake ni banaso, na gwamma ce inyi spending life dina a prison, ka gaya mata I don't need her help, infact i hate her..." xai kara magana yan'sanda suka wuce da ita....
     "gimbiya taja tsaki, ya xaai alkali ya bata 3months kacal, muda muke expecting 20years," hinde tace lailai we have to strike fast, cox idan ta fito prison kashin mu ya bushe, "kedai bari ai banga ta xama ba, cikin wata ukun nan xan cika burina in waske, bazaku kara gani na ba, " hinde ta balla mata harara, kardai ki manta idan kudin sun samu 50-50 zamuyi, "eh mana tawan raba dede xaai...." baba shehu ko ajikin shi, sam bai damu ba, yasan kota pito prison bazata doso gidan ba..

Gaskia we have to do sumtym, dan baxan yadda ta fito so soon ba, am very sure har yanxu ya yazid nasonta, idan ta fito am finished, "meerah dake saura ranta tace calm down, miye kike tada hankali akan minor abu,  nariga na mana planning komai, today will be her last day on earth
    " zee tace bangane ba, wana plans kikai ???
      "ta kwashe da dariya, akwai wata prisoner da guy dina ya hadani da ita, naje munyi magana na nuna mata pic din kursum, ita nakeso akashe koda ta dawo prison din, kinsan mi tace da taga pic din...
       " a'a gaya min...."cewa tayi itama she has been targeting her, cox akan kursum sai da tarasa ido daya tsananin marin da wata tai mata..
     "Zee tayi murmushi tace galfrnd u are rily smart, killing her is d best option, amma ya sunan prisoner din ???
        " I dunno her real name, nasan dai ana kiran ta da Snake🐍🐍🐍.......

*Xarah Abubakar*😊
*Dedicated to Badia*

~luv u oll~😘😘
[04/10 6:12 AM] 💕: *KURSUM*

          By ~ Xarah Bukar

6⃣9⃣✨

kara k'cewa da daria   sukai daga bisani suka
tashi suka fice, ta ajiye meerah agida sannan itama ta wuce gida
     "abba da umma na dinning suna lunch, ta shigo ayatsine, ko kallan su batai ba ta wuce daki, " umma ta nisa, kaga halinta ko, sam batasan darajan mutane baa...."hannu abba ya daka yace dakata plz, ya kamata kina mata uzuri na tabbata bata lura damu ba, uhmm umma tayi tai shuru
      "qwas!! qwas!! ta dawo
Palon, suka bita da ido👀....ta karasa dinning  ta zauna tare da binsu da kallon banxa tace ina husby na ban gan shi ba...." dakyar abba yace baya  nan na tura shi wani aiki abuja da safyn nan, bai gayamiki bane ??
       "tace kaii matsala ta da tsappi kenan, sai bakar munafunci, ya'xaai ya gayamin tunda uwarsa naima kai take dani, " akufule abba ya kalleta, kina da hankali kuwa, mu kike zagi ??
     "taja tsaki tare da mikewa tsaya, kudai ku kasani, tafiya ta xanyi idan yadawo kwa ganni, fuuuu ta fice...." umma ta girgiza kai,uhmm yaudai ka gani da idonka tun baa je ko ina ba, yace lailai kam nagani, amma kyaleta kawai, taci darajan amintakar dake tsakani na da marigayi  alhaji tanimu dayau na raba auran nan, "aranta tace Allah sarki, ita kursum da baka kauna ba kasan itace diyar saba, afili tace sai hakuri, yaran yanxu sai fatan shiriya....Amin kawai yace yay shuru dan ba karamin shaka yay ba..
     " umma tace "munyi magana da huzaifa,
       akan mi ?? ya tambaya....akan kursum, wata uku xatai a akurkuku, ka taimaka kabarni in dubota ko sau dayane, ga hanifa sam bata da sukuni rashin ganin uwarta, "yace toh naji amma ba yanxu ba...

Abuja

Zaune yake a hotel din daya sauka ya bude suitcase dinshi ya ciro wasu papers yana duba wa, yaci karo da dairy dinta, ya bude first page, ba wani rubutu masu yawa bane, ya karanta:
       " I liked yhu from d first moment I saw u, when I declared ur love I kept it in my mind cox it was one of the happiest dayx of my life, dou yhu came to me to brighten my life, tanks to u I knw wat to be truly loved it is. All d words in the world are not enough to tell yhu......I love u so much yaya yazid, "I hope one day u will find a place in ur heart to 4give me of all my mistakes.......
         "Jikin shi yay sanyin, ya rufe da sauri ya ijiye, yace anya banyi kuskure ba, yay saurin kawar da tunanin, ya duba fone dinshi yaga 10missed calls na zee, tsaki yaja  ya kashe wayar, aikin sati biu yakawo shi amma sai ya cika wata guda kafin ya koma, ya mike tare da kwashe papers din ya wuce office

Kano

Kinyi daidai da kika baro gidan kika dawo nan, dan kin damu dashi datx y yake miki bura ubar daya ga dama, tsabagn askanci da rainin wayo yasan  xaiyi tapia shine bai gayamaki ba, "zee dake zaune ciki da takaici tace kedai bari, ai harda hadin bakin iyayan, Sam basu dauke ni da daraja ba, meerah tace  shiyasa nace  ki rabu da yazid basonki yake ba, atleast choose sumtn good in ur life, ga olamide tun muna skull yake bibbiyar ki kinki kula shi, yanxu haka ya shigo kano, yana ma hanya zuwa nan
      " kina nufin na ajiye aurena aside in kula shi kenan ?? "a'a, auranki na nan mana, zafi kawai zaki rage tunda shi mijin is not ready....." zata kara magana suka ji knocking door.....meerah ta tashi ta bude, da fara'arta tace olamide long time, "yayi dariya ya karaso ciki, ganin xee zaune tayi kicin kicin yasa shi kara darawa yace my love baza kiyi wlcmn dina ba, " harara ta wurga mai taja tsaki, ita dai baya burge ta Sam...."meerah tace don't mind her, zauna barin kawo mana solution, ta shiga daki ta kwasa masu giya kusan kwalba takwas ta diri masu, ola yace wow kinsa na tuno da scul yadda muke baje wa asha ayi tatil, "hhh aifa dole mutum yay enjoying life kafin ya tsofe, " tsaki zee ta kuma ja sannan tadau bottle daya tafara kwankwada, ola ya dan saci kallonta yana murmushi

Akufule ya kalleta, ashe baki da hankali, kujerar M.D danai shekara da shekaru ina naima, yanxu nasamu shine zaki xo min da xancen banxa wai kema m.D din kikeso, ke asuwa ?? toh wlh baki isa ba...."tayi shewa tace shehu baa ja dani, ko ka bani m.D ko kuma in tona asiri kai kasa nawa kursum shairi, "ya kwashe da dariya, kinyi blackmailing dina d first tym na kyaleki, diz tym saidai kiyi abunda xakiyi cox it won't work, infact zaman ki gidan nan it over, pack ur tinxx n leave
      " gimbiya tayi tsuro, tabbas inta biye mai xai iya wurgi da ita, ta marairace fuska tace haba shehu mai yayi zafi haka, kayi hakuri wasa fa nake...."ya wurga mata harara, nidai ina baki warning, if yhu try anytn stupid jikin ki xai gaya maki..."yaken dole tayi tace toh, ta koma dakinta rai bace..
      "hinde dake zaune ta taso da sauri, lapia dai koh ??  ta kara tamke fuska tace nayi iya kokari na I don't tink xai bada hadin, hinde tace akwai matsala kenan, " kwarai kuwa, xan kyale shi 4 now, sai komai yayi sanyi zamu mai d hard way...

Prison
1.46am

Dare ya tsula wasu har sun kwanta, banda kursum dake zaune cell din lady suna hira, "lady da akema kitso tace it seems gimbiya nan bakin su daya da baba shehu datx y suka hada baki wajan miki karya, " kursum tace nasan halin gimbiya, she cnt be trusted, am sure tana da wani hidden plans akan shi, "Lady tayi kwafa, ai wasu akan kudi dey can do n undo..
     Ta tabo mai mata kitso, ke maza ceki laundry room ki dauko min towel dina, tace toh....." Kursum tayi caraf tace a'a ku cigaba da kitson barin je in dauko, lady tace okay b carefully
      "Hankali kwance ta mike ta fito, tana tafe  wani shadow na binta, sam bata lura ba, ta shiga ta dau towel din, xata  fito kenan taji an shake mata wuya tabaya tare da toshe mata baki, atsorace ta kwalalo ido, tana kokarin magana takasa.....
     " ganin shadow din zungureren wuka yasata gigicewa.......

*Xarah Abubakar*
*Dedicated to Badia*

Xarah's Novel📝
[04/10 6:13 AM] 💕: [03/10 9:16 pm] Xarah✍🏻:
*KURSUM*
 
         By ~ xarah bukar

7⃣0⃣✨

Dakyar ta kwace kanta tana hakyy, ta juyo agigice, ganin snake rike da xungureriya wuka fuskar ba annuri yasata kara kidi mewa, "snake tayi yake ta karaso tab da ita ta matse ta a bango tace ko kinyi ihu bamai ji balle ki xata  xaa ceceki, daga ni sai ke...kiyi hakuri ki kyaleni plz....ta hauta da kakkyawan maruka ta ko wana angle a fuska, baki har yana zubda jini,
       "Baki na rawa Kursum tace antee snake dan Allah karki kashe ni kiyi hakuri ki kyaleni plz...." hhh tunda kin shigo hannu dole kibi ancestors, ta dago wukan zata caka mata suka ji anturo kofa an shigo, atsorace tayi wurgi da wukan ganin lady tsaye ba annuri tare da prisoners guda uku..
       "aguje Kursum ta karaso gurunta tana kuka, ta kalli fuskan ta dayay ja ga jini na xuba ta hanci da baki, tace pretty who did this ?? kasa magana tayi, saima kukan dayaci karfinta....." Ran lady ya baci matuka, ta karasa wajan snake datai tsuru tsuru gabanta na dukan uku-uku, ta shakota, dint I warn yhu to stay away from my property, "murya na rawa tace ba lafina bane I was just following orders, ta kara tamke ta, orders 4rm who ?? ....uhmm I dunno knw her name, munyi da ita kawai zata biyani idan nakashe pretty..." Lady tace datx good, ta kira daya daga cikin guards dinta tace bani wukan nan, ta mika mata, oya Ku rike min ita gam ku bani hannuta "akidime snake tace mi xaku min ?? lady tace alkawarina xan cika, ta dauki kayan dake wajan ta daure mata baki tamau sannan tasa wuka ta kille mata two fingers kattt kattt ....😳😳ba snake kadai ba hatta Kursum dake gefe saida ta tsorata ga jini sai tsiyaya yake
      " snake dan azaba sai mukursusu take tana zubda hawaye, ga baki an tamke balle tayi ihu kotaji dan dadi..."lady tace kadan namiki yanxu buh next tym am gonna cut off ur head, ta kalli guards din tace ku  gyaran wajan sannan ku kaikai ta clinic ayi treating dinta, ke kuma ta nuna snake da yatsa idan an tambaya hw cms, cewa zakiyi u had an accident wen closing d doors..
      "Da sauri snake ta daga kai tace yes, I had a terrible accident, " tayi murmushi tare da ja mata cheeks, yauwa good gal ashe kingane......taja hannu Kursum suka bar wajan

Suna zaune tana goge mata fuska tace acikin su wa kike ganin ya bada order akashe ki, dan yadda snake tayi magana am sure mace ce, "Kursum ta sauke dogon ajiyar zuciya, I dunno, amma ina suspecting mutum uku, gimbiya, zee ko hajiya, " lady tace I don't tink hajiya nada wani motives akanki, tunda kince ba wani cikakken lapia gareta ba, ni aganina zee ce  cox ita keda reason din kawar dake, tace hakane fah, koma dai miye Allah ya fisu, tankx  to yhu am alive

Da safe
10.42am

Farkawa tayi tare da mika, ta yunkuro xata tashi taji wani irin azababben ciwo tsakanin cinyoyinta, ta dube jikin ta dako kaya babu , afirgice ta daga com4ta data rufa dashi  takara tsorata ganin aika aikan daya wanxu, ta duba gefe, yana bacci hankali kwance, ta daddage ta daka mai duka, tsum ya tashi akufule....miye haka ??
     "a hasale tace ola wat did u do ??
      yay dariya, excuse me wat we did zaki ce, kokin manta ne...." tayi shiru tana son tuna abunda ya faru, ita dai tasan last nyt she was drunk, amma ina meerah take ? hw cms na dawo daki ??
     "ta kalle shi araunane, I cnt  biliv u took advantage of me.....yace my love kar kice haka plz, u knw I love u..." ta wurga mai harara, yhu stole mah virginity, I hate u n I'll neva 4give yhu....ya matso xai tabata, tayi ihu tare da wurga mai pillow, don't u dare touch me, infact i dnt want 2 c ur face again, just pack ur tinxx n leave...."yay shuru yana kallon ta daga bisani ya tashi yasa kayansa ya fice
     "Meerah ta shigo da saurinta, zee miya faru naga ola ya fita rai bace, " ta harareta, don't play dumb ai kinsan abun da ya faru, tace ohh nikam bansan Komai...
    "kar kimin karya just tell me wat happen last nyt.....ta nisa tace nima I cnt  recall nasan dai we wia all drunk, bansan hw cms kuma keda ola kuka fara smooches, ni kuma daga nan I slept off...
     " ta buga uban tsaki, wlh ya cuceni, I wantd mah husby to be my first, amma shegen nan yaxo yamin basaja, "meerah tace calm down, miye aciki atleast yanxu kin zama big gurl, ni yanxu fita xanyi amma barin hada miki hot ruwa ki gasa jiki....Ina zaki ??
"tace xanje ganin snake ne, kinsan ya kamata musan kota cika aiki, zee tace gaskia ne Allah sa a samu good news, " ta kece da dariya, don't worry, just chill up, yanxu xanje in dawo...

Prison

Kursum ce zaune da inna a visitors space, inna tace munyi waya da umma ta na gaida ki, hidima ya hanata xuwa, tana samun lokaci zata zo....."tace ba komai ma, umma ta nuna min kauna saidai Allah ya saka kawai.            "ya akai fuskan kin kumbure, an miki duka ne ??
    "tai murmushi, ba komai fah bugewa kawai nayi, ya hanifa??
Inna ta numfasa tace uhmm tana nan kalau, nida  uwarta tamin rashin M, ta koreni daga gidan..." kwalalo ido tayi tace wace uwar ??
      "Zainab mana, matar yazid din...agigice tace sunyi aure ne...." eh mana, ai baa daga auran ba, da ita akai.....innalillahi wa inna'ilaihi raji'un ta furta a tsoroce, tace shi kenan inna kashe min hanifa xatai...."karki damu baa abunda ta iya tunda umma na nan, mudai fatan mu ki fito lapia, "jiki asanyaye tace nifa kona fito banda gidan zuwa, inna tace ahab gida ba matsala bane, kinga ni gobe xan koma bauchi, xan iya bar miki mukullin gidan da nake, saiki yi zaman ki can...." nagode sosai inna, gaskia kin kyauta min, Allah yabar zumunci, tace ba komai wlh, nima kin taimaka min lokacin da babu..
      "Murmushi Kursum tai,tayi shiru tana mamakin irin kiyayyan da ya yazid ke mata, koma dai minene tasan ita yakeso ba zee ba, zata bashi tym harya huce
     Suka cigaba da hira daga bisani inna tai mata sallama ta tafi....

Ta tashi ta koma ciki asanyaye, sukayi kicibis da snake zata shiga V.s, ta kalli hannuta daya sha bandage abun tausayi, da sauri taja gefe taba kursum hanya ta wuce, dan ba karamin tsorata tai ba...." ta karasa v.s ta zauna, meerah dake jiranta ta kalleta ayatsine, ke kuma lapia naga hannu daure ??
     "Snake tace ke aiki bai yuyuba fah cox sum1 is protecting her, yanxu haka saboda ita nayi loosing two fingers....." ta kwashe da dariya, u'r so stupid, dan aikin nan kika kasa, mtsww
     "snake tace don't insult, xan baki contact din bro dina ki bashi kudin aiki....." ta balla mata harara, ai babu balance tsakani na dake, wana aiki kikamin ???  "tace ban miki aiki ba,amma akan aikin komai ya dawo kaina, dan haka u must give me sumtn..... meerah tace u are not serious, ko anini baki samu, kinga tafia ta, ta mike tsaye ta wuce abunta...." snake dake zaune rai abace ta mike ta koma ciki, aranta tayi alwashin daukar fansa akan meerah komin daran dadewa....(hhhh😂😂😂)

*Bayan wata Daya*

Gimbiya da baba shehu an shirya kaman gaske, suna kan dining suna breakfast, baba shehu yace wai hajiya bata kira ki bane..."tace eh jiya ta kirani tana gaida ka, inda sukene ba network mai kyau...."yace no wonder bana samunta idan nakira,
     "e wlh, nan da wata uku ko hudu zata dawo...ya nisa yace Allah sa dai lapia, dadewar tayi yawa, nizan wuce office idan tasake kira kice ta naime ni...." gimbiya tace toh aranta tace saidai wata ta kira badai itaba😖😖

Umma ce tsaye a daki ta goya  hanifa dake kukan bacci, kusan wata daya kenan tana cigiyar hajiya ba labari, ance taje zamfara har yanxu shuru bata dawo, har gidan  taje aka hanata shiga wai gimbiya tasa doka kar ashiga, "taji wayanta na ringing, ta duba taga yazid ne, da sauri ta dauka...
       " suka gaisa lapia lau, dan yanxu ta rage fushi, tace my son ya kamata dai ka dawo, I miss u alot.."yace gobe xan dawo umma, ya hanifa, hop dai zee na kula da ita....tace uhmm hanifa is fyn, matar ka kuma banda case da ita, so karma ka tambaye ni ita, "yace sorry my umma, ya labarin kursum ?? tace ina ruwanka da ita, I tot u said she ix dead to yhu..." Just asking kawai, tace don't ask plz, kuma ka tabbata ka dawo gobe, ta katse wayan......
     "yay shuru yana kallon wayan, umma CE kawai yasan  tasan labarin ta, ya sauke ajiyan zuciya, yace tabbas salma zata sani, ya duba contact babu no dinta, yay tsaki, da kunya kuma ya kira huzaifa ya tambaye shi.....haka dai ya zauna shiru asukwane

Suna zaune Doctor ya shigo da result, ya kalli zee data fita hayyacinta kwana biu yace congrat madam u'r one month pregnant, meerah tace haba dai doc kodai result din wata ne, yace a'a, yamika mata paper,karanta da kanki....ta duba, ta tabo xee ke dagaske nefa...."akufule zee ta tashi tayi waje, gaba daya hankalinta ya tashi, " meerah ta biyo ta aguje tana kiranta, tayi banza da ita...suka shiga mota, taja afusace, "galfrnd take it easy mana, so kike muyi accident ne, " dakyar xee ta  iya cewa kyaleni kawai inada unfinish bizness da Kursum, tunda bata mutuba I have to try sumtn new....."tace okay oooo, nidai xan jiraki a mota.....
     Suna isa tayi parking agurguje, ta shiga da sauri ta......
       Tana zaune security guard yaxo kiranta tayi bakuwa, ta fita zuwa v.s tana mamakin ko waye, kusan wata daya kenan ba Wanda yaxo......tana zuwa taga zee CE,tace sis yau kin tuno dani ne, "ta wurga mata harara, nazo baki warning, koda kin fito karki kuskura kice zaki nemi ya yazid, dan yanxu haka ina dauke da cikinsa na wata daya.....plz ina rokanki stay away from us, yadda hanifa bata rayu da uwarta ba karki sa dan cikina ya rayu ba da uban saba, ki taimaka plz......ko jiran amsan Kursum batai ba, ta juya ta fice......itama kasa tashi tayi banda zubda hawaye da take, wato ya yazid har ya manta da ita so soon, tayi alkawarin hakura dashi koda sonshi xai kasheta....

Ba wanda yace uffan har suka dawo gida, suka zauna Palo shiru daga bisani meerah tace waike xee miye haka, kinyi shuru tun dazu, ta nisa tace mi xance toh...diiinn taji karar msg ya shigo wayanta, ta duba, msg ne daga ya yazid, da sauri ta karanta...."ta dago agigice ta kalli meerah, oh my God ya yazid is coming baq 2moa🙆🙆�, tace toh sai mi dan xai dawo, "akidime zee tace na shiga uku,INA dauke da cikin olamide taya xan koma gida....." tace abu mai sauki ayi aborting kawai....caraf akunnen ola dake tsaya bakin kofa yana shirin shigowa.....ya karaso yace babu wanda xai kashe min DA Ina Raye.......
    "atsorace suka juyo suna kallon shi😳😳😳

*Xarah Abubakar*

Xarah's Novel📝📘

2 comments:

  1. https://mynovels.com.ng/jiki-na-yake-so-complete-hausa-novel/

    https://mynovels.com.ng/sadauki-omar-return-complete-hausa-novel/

    ReplyDelete