Friday, 14 October 2016

Kursum 31 to 40

🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
     
       🌺🌺   By ~Xarah Bêê

Page 3⃣1⃣~ 3⃣5⃣✨

Kursum ta farka taganta a gadon asibiti, duk jikinta ya kurje ga farin bandage da aka daura mata a kai dan tsayar da jinin dake zuba, sai kuka da ihu take tana Kiran sunan sumy.
Da gudu wanda ya tsince ta a hanya ya kawota asibiti yaje ya kira doctor malik yana gayamai patient din ta tashi amma kaman bata hayyacinta...
Doctor ya shiga yana mata magana, amma ita kam ihu kawai take tana Kiran sumy, ya tsira mata allurar bacci ya fito.
Yace Bala daka tsince ta babu waya ahannunta ko wani abu dazai sa musan family dinta ko inda take zama, Bala yace gaskia babu sai dai ko jakarta xaa duba, dan koda na ganta akwai karamar jaka tare da ita, ya mikawa doctor malik jakar, suka zazzage jakar daga kayan kwalliya sai wani wallet mai kyau suka bude, pictures din daddy kuda biyu Dana kursum ne aciki sai wani karamin littafi an rubuta sumayya tanimu bawa.
Doctor malik yace ai wanan hoton alhaji ne, kuma ba shakka wanna yarinyar yar'sa ce amma to ina taje harta samu accident, ya kalli Bala yace mungode sosai da taimakon da kayi,  nasan family din yarinyan kuma yanxu zan kirasu awaya suzo su dauketa, nine family doctor din su. Bala ma yamai godiya sannan ya wuce.
Doctor malik ya kira mummy yamata bayanin komai, tace tabbas yar'ta ce dan dama tun wajen kwana biyu daya wuce akaje dauko ta daga makaranta, amma sukaji shiru basu iso gida ba, an duba hanya an gano motarsu tayi hatsari ta kone sai gawan mutum biyu akone kawai aka gani, kuma ance mana tare suke da kawarta daga makaranta, doctor yace kawar ce ta rasu da driver kenan, dan yanxu haka sumy na nan kuma jikinta yayi sauki sai dan ciwon da baza'a rasa ba, tayi mai godiya sosai tace zata turo baba shehu yaxo ya dawo da sumy gida..

Kursum ta tashi sai dai ba ihu yanxu sai kuka kawai take, doctor ya shigo yana gayamata ai kawarta da sukai accident tare ta rasu dan haka yanxu ta shirya kanta dan kanin mamanta yazo daukanta suje gida, ya dauko wallet da pictures din yabata hade da jakan gabadaya sannan ya bata magunguna wanda zata sha, yace sumy ki tabata kinsha maganin nan saboda your body is still weak, tace to nagode sosai doctor, Kursum kam hankalinta duk ya tashi shikenan sumy ta  rasu yanxu ya zata yi , gashi kuma ana tunanin itace sumy alhalin kuma sumy ce ta rasu ba kursum ba, amma kuma dole ne ta tsaya a matsayin itace sumy kodan ta samo wa hanifa gata da yancin ta.

Ta fito ta iske baba shehu na jiran ta, dukda batasan shi ba saida tace kawu ina wuni, ya bita da kallon banza sannan ya amsa a kwasale yayi gaba abunshi tana binshi a abaya,  a zuciyan ta tace tab wato family dinnan babu sauki, lailai zata daura damara dasu dan kuwa baza tai tolerating ko wana nonsense ba.

Suna isa gidan yayi parking mota suka fito, masha Allahu kawai take fada dan kuwa bata taba ganin katon gida mai kyau kaman wannan ba, wani tausayin sumy taji, Allah yaji kanki kawata kuma insha Allahu hanifa sai ta samu gatan xaman gidan nan Daram. ...

Hajiya da xee suna zaune a parlour suna jiran isowan su sumy, baba shehu yafara turo kofa sai kursum abaya,  tana karasowa cikin palon xee da mum suka tashi tsaye afirgice suna kallon ta.......

Nima afirgice nayar da biron rubutuna dan na tsorata da yanayin mom, ita da bata gani miyasata firgita haka..😳😳

             *Xarah Bêê*
          
*Dedicated to Bady social*
         
       ~Luv u all~😘😘😘

🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
     
        🌺🌺   By ~Xarah Bêê

Page 3⃣6⃣ ~ 4⃣0⃣✨


Kursum ta dukusa har kasa ta gaishe su, hajiya kam hankalinta bai tare da ita, mamaki kawai take yadda sumy ta zama kekkyawan budurwa dan koda tasan ta abaya ba wani kyau garetaba sai fari kawai .......abangaren xee kuwa faduwan gabanta sai karuwa yake, yaudai duk takama da kyawuta taga Wace ta fita kyau da komai, wani irin tsanar kursum taji azuciyanta. .......😡😡

 Hajiya amsa adakile, ta kwallawa samira kira, taxo da sauri tana gani hajiya, tace kikai sumy can gidan baya kusa da dakin masu aiki sai ta zabi dakin data ke so, samira tace toh.

Kursum da haushi hajiya ya isheta ta, ta karaso cikin palon ta xauna tace tunda gidan ubana ne babu wanda ya isa yasani xama dakin masu aiki, dan haka nima a main house zan zauna, ta tambayi samira ina dakuna suke da kuma wana dakine yafi kyau da girma a gidan, tace antee dakuna asama suke kuma dakin daddy yafi kyau da girma tunda ya rasu babu wanda ya shiga,  kursum ta mike tsaye ta karewa hajiya da xee kallon sannan tace samira kaini dakin daddy dan yanxu yaxama nawa in ga wanda ya isa ya hanani...😕

Hajiya kaman tafasa ihu 😫😫 dan takaici, lailai yarinyan nan wato ba kyau kadai takara ba harda baki tayi, yazama dole insa mata ido saboda.....

Da daddare Abba da umma ke zauna a parlour sai hira suke suna darawa, umma tace gaskia yakama in leka hajiya mun dade bamu haduba aiki yamin yawa.
Abba ya kalleta yace wai ke bana hanaki shiga harkar hadiza ba, kinsan sarai banason matan nan saboda Sam bata da mutunci, kowa yasan itace sanadiya mutuwan mijinta , umma tace haba alhaji ya za ai kace haka, lokacin mijinta ne yayi....... bata ida magana na ba yazid ya shigo da sallaman sa, sanye yake da uniform dinsa na pilot wanda ya kara fito da ainuhin kyau shi, ya fada kan kujera yana wai na gaji, umma ta kalle shi tace my son hope dai you are okay, banason ganinka da stress , Abba yayi tsaki yace wlh maryam ke kike kara sangarta yaron nan, idan baije aiki ba so kike yana xaman gida ko me, shida wataran zaiyi aure ya kula da iyalansa......yauwa nama tuna shehu yazo min da batun diyar shi Zainab dinnan kwana kin baya,  kun dade kuna soyyaya amma baka ma xancen aurenta kuma ma dai at your age ya kamata ace kafara tunanin fara iyali.

Yazid ya tamke fuska, yace gaskia abba ni ban shirya aure ba dukda inason xee, koda zanyi aure sai nan da shekera daya, ya tashi a fusace ya wuce dakin shi.

Abba ya kalli umma yace kinga halin son dinki ko , tace karka takura mai tunda yace ba yanxu ba, ni xee dince ma banaso ya aure Sam bata da kamun kai, yace to ina ruwanki bashi ya gani yanaso ba kuma ni banga rashin kumun kan taba, babanta abokina ne kuma yana da kirki sosai,
umma dai shiru tayi bata ce komai.    

***************************

Bayan kwana biyu jikin kursum ya warware ta samu sauki sosai tayi fresh ta kara kyau, sai dai zaman kadaice da take babu mai shiga harkanta a gidan sai samira kawai dan ita ke kawo mata abinci har daki, tayi tsaki ta kwallawa samira kira,
taxo da saurin ta tace antee kina bukatan wani abu ne, kursum tace babu komai tambayan ki zanyi wai babu masu shigowa gidan nan ne, naga tunda na zo banji an shigo ba, gida sai kace kurkuku......samira ta gyara zama tace antee ai indai gidan nan ne ana wata biyu babu wanda ya shigo, yaya yazid kadai ke xuwa wataran umman shi takan zo wajan hajiya dan kawarta ce sosai,
kursum ta nisa tace Waye kuma yaya yazid wajan wa yake zuwa, samira tace ai saurayin antee Zee ne kuma suna son junan su sosai bare ma antee zee tana iya mutuwa akanshi,
kursum ta bata rai tace tashi ki fita ban tambayi ki wannan ba, sumsum ta tashi ta fice da saurinta......ita ko wani farin ciki taji ta maimaita sunan yaya yazid, gaskia sunan ya mata dadi. .. 😀😀

Da yamma barrister shu'aibu yazo har gidan ya damkawa kursum takardun gidan da komai data mallaka amatsayin itace sumy, sannan yace mata ta shirya gobe zata fara aiki acompany din babanta amatsayin managing director, tamai godiya sosai ya masu sallama ya fice.

Hajiya dake gefe sai hararan kursum take ta eye glass dinta (oho dai batasan kina yiba)......😜😜😜
Baba shehu ma ya cika yayi fam 😜😜😜, ya kalli kursum yace yanxu sumy abunda ya kamata shine kibarmin komai a hannun na tunda na dade in charge, xan naima maki admission ki shiga university tunda iya kacinki secondary skull kuma baki da experience na managing babban company,
kursum shiru kawai tayi batace komai ba ta haura sama abunta. ....
 Baba shehu yayi murmushin samun nasara da alaman yarinyar ta yadda da Zancen shi....😀😀

Washe gari da safe kursum ta shirya cikin hadadden pink and white suit mai shegen kyau na kardashian collection tayi rolling kanta da karamin pink veil mai kyau, ta dauki handbag karamin mai kyan gaske mai tambari versace tarike a hannu, tabi stairs tana sauka atsanake hankalinta kwance, ji tayi an bangajeta har tana naima fadowa kasa, tana daga kai tayi ido hudu da xee, da ganinta kasan she is high danko kayan jikinta bana kirki bane,
xee tace ke dabbar ina ce ko bakiga ina hawowa bane, banza bakauya taja tsaki ta wuce,
kursum kasa cewa komai tayi ta wuce abunta tana mamakin hali irin na xee ta tabbata daga club take kuma till dawn tayi, dan samira ta taba gayamata xee bata fiya kwana agida ba, bata da aiki sai clubbing, kuma baba shehu da hajiya suna sane amma babu mai kwabarta....
Allah ya shiryeta kawai tace ta karasa waje ta shiga hadaddeyar motar ta kirar 2016 Buick Cascada..........driver yaja ta sai company.

Babban Company ne mai huge twenty-story office building, all curved glass and steel, an architect's utilitarian fantasy, with Tanimu bawa oil & investment written discreetly in steel over the glass front doors.
Tana shiga officials din suka karaso suna gaishe ta tare da mata congrat as the new MD , ta amsa da fara'arta tana masu godiya, Mr dabo ya karaso gabanta yace madam am your PA let me excort u to ur office,
ta bishi har office din amma sai tayi mamakin 😳😳 ganin office karami kaman gidan kaji, ta juyo tace Mr dabo how comes ina MD zaa bani karamin office haka,  yace madam kiyi hakuri ba laifin mu bane, kawunki yace abaki nan tunda ba wani sanin kan aikin kikayi ba,
kursum tace lailai ma baba shehu wato itace ta dace danan, aikuwa zanyi maganin shi.... ..tace Mr dabo kaini office din baba shehu yace toh...
Suna shiga taga office dinshi tankameme kaman aljarnar duniya komai na office din ya burgeta tace Mr dabo nan nake so as my office ka kwashe tarkacen kawo ka canza mai wani office sannan kuma ka kawo min file din ko wana employee zan fara aiki na, yace to angama madam Ya fice. ... 

Kursum zauna kan office chair tana swivel din kanta, sumy kawai take tunanin, Allah sarki kawata da yanxu kice anan bani ba, Allah yaji kanki insha Allahu zan rike maki hanifa tamkar nina haifeta...

Banko wan kofan da akayi ne ya firgita ta, baba shehu ne fuskar nan tamke, babu annuri ko kadan, yace "I won't let you disrespect me, I've been working day, noon, and night for this company, busting my hump since before you were born." who are you to throw me out of my office?
Kursum ta mike tsaye ta karemai kallon sannan tace, the early bird doesn't always catch the worm, Warming a seat in this company doesn't mean you're working,
baba shehu daya gama kulewa ya nunata da yatsa yace, how dare you, you snot-nosed brat!
Kinsan dawa kike magana kuwa, ta kara kare mai kallo tace, I dare because I'm the heir to my father's company. From now on, I'm going to monitor the performance of every employee; including you. No, not including, but beginning with you. If you don't like it, the door is wide open enough. Understand?  or should I draw you a picture?"

Baba shehu kasa cewa komai Cox kalamanta ba karamin girgiza shi yayi ba, sai yanxu ya tabbatar kawar da yarinyan nan will not b easy, amma dole ne ya naima mafita kafin taza ma doom dinshi🙆🏿

Hmmmm

          *Xarah Bêê*
 
*Dedicated to Bady social*
        
         ~Luv u all~😘😘😘

No comments:

Post a Comment