🌺🌺🌺 KURSUM🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺 By ~Xarah B
Page 4⃣1⃣ ~ 4⃣5⃣
Zaune yake a office dinsa yana waya da xee tana ta zuba mai shagwaba kaman tana gabanshi, ta turo baki tace baby kace zaka zo Jiya baka zo ba I couldn't sleep Cox I was thinking of u kuma your fone was off, ta kara shagwabe fuska, yace am sorry dear I was kinda busy ne xanzo anjima, kar kiyi fushi kinsan I love you alot..........Abba ne ya shigo office din yasamu kujera ya zauna jiran ya gama wayan, yazid yace baby xan kiraki later, tace toh my love, kisses & hugs dear 💋💋......
Abba yace miye amfanin love dinnan da bai da future, ance kayi aure kace you are not ready, kudai yaran zamani halinku sai ku, yayi murmushi yace abba abar xancen auran nan plz, nace muku am not ready, abba yace kai ka sani yanxu dai ga document din shares din mu na Tanimu bawa oil & investment company, Ina so gobe ka kaiwa new MD na company din tasa hannu, ya dire mai document din ya fice abunshi , yazid ya bude yana dubawa yace abba kenan wato dan aikin nan ma bazai tura wani ba dole dai ni zai aika........😡😡😡
Hajiya ce zaune a falo rike da sandar ta, tasha bakin glass dinta, tunanin kawai take yadda za ta fidda sumy daga gidan dan Sam bata yarda da ita ba, tana suspecting akwai abunda take boye masu, tasha leka dan karamin ramin dake jikin kofan dakin ta, ta ganta rike da wani hoto tana kuka tana cewa ki yafeni hakan da nayi shine kadai mafita, hajiya ta tashi da saurin ta haura sama, ita dai tana son sanin wana mafita sumy take nufi, ta bude dakin kursum ta shiga ta fara bude bude da binciken amma bata ga komai ba, side drawer na gadon taxo budewo ta ji muryan samira abakin kofa tana cewa Antee kin dawo ne, da sauri ta maida glass dinta ta fito daga dakin, samira tace hajiya kece aciki ashe, ko kallonta bata yi ba ta bi gefe ta wuce tana dafa bango dan karta fadi........
Samira mamaki ne ya cika ta, matar da bata gani miye na shiga dakin daba nata ba kuma da alama ma bincike take, ikon Allah kenan.....😳😳😳
Kursum zaune a office tana hada files waje daya dan yamma tayi zata wuce gida, ta kira Mr dabo tace mai ya kwashe duka files din ta gama dubasu sannan tamai sallama ta wuce parking lot tasamu driver na jiranta a mota, ta shiga ya ja....🚗🚗
Sun hau kan babban titi driver ya hango hold up sosai, babu alaman motoci na motsi, yace madam hold up dinnan yayi yawa amma akwai wani one way gaba kadan, bari inbi damu tanan, kursum tace toh duk yadda kayi ta cigaba da kallon sabuwar wayar da ta siya dazu kirar iphone 3G king's Button...
Daidai lokacin da driver ya danno kan motar, dai dai lokacin da shima ya karyo kwana sai ji kake kiiiiiiiiiii........ko wannan su yaja birki, kiris ya rage suyi accident..🙆🙆🙆🙆
Sanye yake da uniform dinsa na pilot yasha kyau da alama shima daga aiki yake ya fito fuska tamke, tun kafin ya karaso driver ya fito da sauri yazo yana bashi hakuri, amma ina shi kam baisan hakuri ba sai zazzaga masifa yake yace kai wawan ina ne, koka taba ganin inda akabi one way, hanyar da ake fita shine kake shirin shiga tunda baka da hankali, driver dai sa hakuri yake bashi....🙏🏻🙏🏻
Tana daga mota take jin hayaniyan su, wato driver na bashi hakuri shi ko guy din kara harzuka yake, lailai ko zata yi maganin shi, ta bude kofar motar ta fito da tafiyar ta mai daukan hankali ta karaso ta bayan shi tace Mr man ko Kaine devil himself sai haka, ana baka hakuri kana kara harzuka, toh karka hakura idan titin taka ce sai mu gani, taja uban tsaki, ya juyo a fusace fuskan nan ba annuri, ya kare mata kallo tas yace ni kike gayawa wai maganar banza , ita ko hankalinta bai ma jikinta dan ba karamin tsorata tayi ba, tabbas babu tantama wannan shine wanda sumy ta aura ya yaudare ta ya gudu, sau daya ta taba ganin shi amma bazata taba manta wa da fuskan shi ba, ba shiri ta saita kanta, ta wurga mai harara tace kwarai kuwa dakai nake kai din banza Waye kai da bazaka hakura ba, Driver mu tafi plz karya hakura din yana iya kwana anan tunda hanyar tasa ce, ta juya ta barshi nan tsaya yana mamaki karfin hali irin nata, lailai ko sai ya koyawa mata hankali, ya ga ubanwa ya tsaya mata da har ta isa ta gayamai magana, yayi kwafa yaja motar sa yabar wajen.
Suna cikin mota tana tunani iri iri, gaskia dole ta naimo Mr devil kodan ta koyamai hankali, wato hankalin shi kwance har wani kyau yakara, kibiyar tsanar shi ce ta soki zuciyar ta, tayi murmushin mugunta afili tace count down to my revenge has ended, it's time for pay back Mr devil......👹👹
Driver yace madam mun iso fah naga kinata magana ke ka dai, tace ahh ba komai barin sauka saika gyara parking, yace toh.
Ta turo kofar parlour da sallaman ta, hajiya da xee na zaune ko kallo bata ishe su ba, tana gaishe su ko amsawa basuyi ba suka bita da harara, ta haura sama abunta....🏃🏻🏃🏻
Xee da taci uban kwalliya da wasu matsasu kayan dake jikinta, ta kalli hajiya tace ni wlh na tsani yarinyan nan ga shegen kyau kamar aljana, ni wataran kina min kama da ita ma, hajiya taja tsaki tace ke daina hadani da mayya ni kaina na fiki tsanar ta, na gayamaki tsinto ta Alhaji yayi a titi, ko jini ban hada da ita ba........zata kara magana hajiya ta tsayar da ita, tace surutun ki ya isheni haka, ba kince saurayin ki zai zo ba, toh sai kiyi zaman jiran shi ai, nikam na tafi daki......xee tace haba hajiya ki tsaya ku gaisa mana, tace nikam bacci zanyi ta haura sama abunta.
Tun komawar shi gida, sallah kawai ya iya gabatarwa, ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi, abunda ya faru dazu gani yake tamkar a mafarki, wai yau shine little witch (sunan daya laka mata ) tama rashin M, lailai ko saiya making life dinta miserable sai tayi dana sanin cin zarafi da ta mai, wani irin tsanar ta yake ji, ya mike ya naushi bango a fili yace Game on little witch..........😡😡😡
Hmmmm tashin hankali🙆🙆🙆🙆
Masu karatu muje xuwa.....
🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺
🌺🌺 by ~ Xarah Bêê
Page 4⃣6⃣ ~ 5⃣0⃣✨
Tana shiga dakin ta ganshi a hargitsi da alaman an shigo an mata bincike, ta kwallawa samira kira, taxo da saurinta tana antee har kin dawo kenan, kursum tace waya shigo min daki naga komai ba daidai ba, samira ta sosa keya tace Antee nima bansani ba amma dai naga hajiya ta fito daga dakin dazu....
Kursum tace hajiya kuma, ita da bata gani miya shigo da ita dakina, tayi shiru can dai tace tashi ki tafi zan naime ki anjima, samira ta tashi ta wuce.....🚶🏿🚶🏿
Ta tashi ta gyara dakin ta kimtsa komai daidai , sannan ta bude side drawer ta dauko picture dinta ita da sumy da pink diamond dinta wanda su kadai ta tsira dasu ranar da sukayi accident da yake cikin aljihun trouser dinta tasa su, ta kalli pic din tana hawaye, rayuwarta da kawarta kawai take tunawa, tayi missing dinta sosai , yanxu tunanin ta daya shine yadda zata dauko hanifa daga Bauchi, ta tashi ta dauko wani karamin book din sumy inda Inna sadiya ta rubuta masu number ta akan in sun iso zasu kira ta, da sauri ta kwashe lambar tayi dialling.........ringing daya biyu Inna sadiya ta dauka da sallaman ta, kursum tace Inna ina wuni ya gida, ya hanifa, nasan baki gane mai magana ba kursum ce.....Damm gaban Inna ya fadi gaba daya ta gigice dan bata taba tunanin kara jin muryar kursum ba, tace kursum dama baki mutu ba , aini dana je aiki makaranta gimbiya ke cemin ai kunyi hatsari kin rasu, kursum tace eh wlh munyi hatsari amma sumy ce ta rasu bani ba.
Inna tace Allah yaji kanta, yanxu hanifa ta zama marainiya, kursum nace haba Inna kar kice haka, nice uwar hanifa yanxu bazan taba bari tayi maraici ba, insha Allahu dana samu lokaci xanzo in dauke ta, Inna tace to babu damuwa sai kinzo, gatanan kuwa tayi bubul da ita, kursum tayi murmushi tace Inna karki gayawa gimbiya ban mutu ba, kibarta amatsayin ni na rasu ba sumy ba, Inna tace toh duk yadda kikace, sukayi sallama ta ajiye wayan.....
Driving yake hankali kwance, fuskar shi ba yabo ba fallasa, yasan rigimar zee idan baije wajen taba zai sha mita, ya iso gidan mai gadi ya bude mai gate ya shigo ciki......
xee data cika tayi fam a parlour, sai tsaki take ja, wajen awa hudu kenan tana jirashi ta kira layin shi switch off, ranta duk abace😡😡😡
taji karar doorbell , ta kira samira taje ta duba waye, ta bude ta ganshi tsaye yana mata murmushin, tace yaya yazid sannu da zuwa ashe Kaine, yace yauwa samira ya karaso ciki, tana jin muryar shi ta tashi da sauri tana kukan shagwaba taje ta rungume shi.
yace haba zee kukan mi kike haka, ta kara fashewa da kuka tace ba Kaine kaki zuwa ba tun dazu nake jiranka, yace baby kiyi hakuri yanxu nazo ai forgive me ? Kinji baby na yakara rungumeta tsam yana shafa bayanta, ita ko sai sauke ajiyar zuciya taje..😍😍
Basu ankara ba sai ji sukayi ana tafa masu 👏👏👏
lokacin guda suka saki juna suka juyo suna kallon ta, sanye take da black jeans da yellow top, sauko wanta kenan zata je kitchen ta naima wa kanta abun ci ta gansu makale da juna kaman ba gobe....
ta masu kallon up & down, tagane guy din sarai shine Mr devil wanda suka samu clash dazu, tace lovers of the year duk iskanci da kukeyi awaje bai ishe ku ba har sai anxo ana nuna hali a gida😕😕, shi kam yazid kasa magana yayi dan mamakin ganinta yake for d second time kuma a gidan nan, ta karaso gabanshi ta nuna shi da yatsa tace shameless man haka dai zaka kare da bin mata, dan iska kawai, xee data bata rai jin kalaman da kursum take gaya masu yasata karasowa da niyyan wanketa da mari amma ina kafin takai mata marin kursum ta rike mata hannu gam tace don't you dare sis, jikina yafi karfin duka, kuma am advicing you to stay away from diz man cox he is just using you for his own selfish reasons, tayi tsaki ta wurgar mata da hannun ta wuce kitchen abunta.....💃🏼💃🏼
yazid yace baby ina kuka samo witch 👺dinnan ne, I hate her with passion, she is rude, zee tace diyar daddy da hajiya ce, shegiyar yarinya, mayya, Yar titi, agidan marayu daddy yasa mota, tana school ne sai yanxu ta dawo gida ......😕
ya nisa yace baby barin wuce kawai, am not in a good mood, tace haba yaya daga zuwan ka zaka tafi, indai akan abunda ta fada ne kayi hakuri zan mata magana😭😭, yace sorry zee but I have to go, ya mata peck a cheeks ya wuce rai abace😡
kursum da take hango su ta kitchen ta kara mata rai, ko miye na mata peck kuma in ba iskanci ba, zuciyar ta namata zafi ...... (su kursum da karfin hali, mutum da budurwa shi karya soye )
No comments:
Post a Comment