Friday, 14 October 2016

Kursum 26 to 30

🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
     
       🌺🌺   By ~Xarah Bêê

Page 2⃣6⃣ ~ 3⃣0⃣✨

*Kano*

Mutuwa daddy ba karamin girgiza jama'a tayi ba, mutane da dama sun sanshi da halin kwarai da taimakawa talakawa, Sam ba ha'inci ko xalinci a lamarin sa......mutane sai shigowa ta'aziya suke, baba shehu na daga waje yana amsan gaisuwa...
Hajiya kuka kawai take dakyar take ma iya amsa gaisuwan da ake mata, hajiya mario ce tadawo gefen ta tana kara bata baki akan tayi hakuri addu'a ya kamata tamai bawai kuka ba.
Zainab ma tayi rashin daddy ba kadan, dan daddy ne kadai yake kwabarta da mata nasiha sosai game da yanda tadau rayuwa da zafi, yau gashi tayi babban rashi. Tana kaunar shi tamkar shiya haife ta..
Har gida yazid yaje yama xee ta'aziya, ya tausaya mata sosai dan yasan yadda suka shaku da daddy ba kadan ba, wani irin sonta ya karaji a zuciyan shi....har dakin hajiya yaje ya mata gaisuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa dan yanxu tadan rage kukan nata,  dazai wuce ta bashi sako ya kaiwa mairo tare da shi mai Albarka. ........yazid kam yana jin haushin yadda hajiya ke cewa umman sa mairo sai kace a kauye Ina laifin maryam ma......😠😠😠

Bauchi
Yan makaranta kam sai shirye shiryen xana jarabawa shiga ajin karshe ake babu wasa kowa ya dukufa da karatu, sumy kam  ciki ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe, "Sam bata da labarin mahaifinta ya rasu wata bakwai da suka wuce.
 Kursum da gimbiya kadai suka San da rasu war shi, sunki sanar matane akan lalular da take tare shi. Sun fiso saita haihu sannan su gaya mata.....

Bayan kwana biyu, sumy ta tashi da nakuda mai tsanani, da gudu kursum ta kira gimbiya sukai rushing dinta zuwa hospital , Allah yasa haihuwan taxo mata da sauki ta haife kakkyawan baby gal wanda babu bambamci da ubanta kaman an tsaga kara an karya...washe gari likita ya sallamo su suka dawo...
Ranan suna ba wani bidiri akai ba, duk da gimbiya ta gayyato mutanan ta, yarinya kam taci suna hanifa son kowa kin wanda ya rasa.
Sumy kam sai murna take, ba karamin son hanifa take ba, dan yanxu tama daina jin haushi mijinta  asalima ta yafe mai duk abunda ya mata...tana fatan Allah ya hada hanifa da ubanta wata ran.
Kursum ce ta shigo daki ta kwantar da hanifa da tayi bacci, tace akwai abunda nakeson gayamaki sumy amma kiyi hakuri bamu gayamaki ba tun lokacin saboda cikin ki, Allah ya yayiwa daddy rasuwa tun wata takwas da suka wuce....
Innalillahi wai inna'ilaihi raji'un kawai sumy take furtawa, kuka take na tashin hankali shikenan daddy ya tafi ya barta yanxu bata da wani gata, yanxu ya zata koma gida da zama, dan bata manta da azabar da tsanar da hajiya ke mata ba tun tana karama, hawaye kawai take tana Allah yaji kanka da rahma daddy......Kursum kam tashi tayi tabar dakin dan bazata iya ganin kawarta cikin yanayin da takeba.......itama tasan tayi rashin daddy ba kadan ba, dan shine ya mamaye mata gurbin uban da bata dashi.

*kano*

Gaba daya family din daddy sun hallara a parlour din gidan tare da lawyer (alkali) sa dan karanto will (wasiha) da alhaji ya bari kafin ya rasu......
Baba shehu kam sai murna yake dan yasan dole yasamu abu mai tsoka, dan tun rasuwar daddy ya maida kanshi managing director din oil company dinsa.
Mommy da xee suma suna zaune suna jiran barrister yafara bayani..
Barrister shu'aibu ya fara da addu'an sannan ya fara bayani yace tun lokacin da alhaji yakamu da ciwon zuciyan yasan bazai dade ba,  shiyasa yazo ya sameni ya bani takardar nan, acewarsa duk ranar da baya duniya yanaso acika masa burinsa dake rubuce anan......barrister ya Bude yafara bayani kaman haka
Ni Alhaji Tanimu Bawa na damkawa ya'ta sumayya dukiyata kashi hamsin acikin kashi Dari,  sannan na bata matsayin managing director na oil company dina da kuma gidan da muke ciki duk na mallaka mata su. 
Acikin kashi hamsin daya rage na bawa hajiya hadiza kashi ashiri, kashi goma na bawa Zainab, kashi goma na bawa shehu sai sauran kashi goma akai masallaci da gidan marayu.
Ina fatan iyalaina zasu cikamin burina , sannan banyi haka danna matawa wani ko wata rai ba.....bissalam

Barrister ya gama karantawa sannan ya mikawa mommy takardar, yace alhaji yamai xancen nan da shekera daya atura driver yaje ya yaje ya dauko sumy daga makaranta, mommy tace to insha Allahu xaai haka, barrister yamasu sallama yatashi ya tafi.

Baba shehu kam fuskan nan babu annuri ko kadan, wato haka alhaji zai sakamai duk irin kokarin dayama company dinsa shine zai bashi 10% kawai acikin uban dukiya daya tare, kuma harda ba yar'sa director din company din, yarinya karama da komai bata sani ba, "Yayi murmushin mugunta da tunanin halaka yarinya kafin ma ta shigo gidan nan..  
Hajiya kam bata damu da abunda tasamu ba asalima abun duniya bai dameta ba, takai cinta daya shine yadda alhaji ya bawa sumy komai daya mallaka alhalin bama yar'sa bace ta jini, zata bar sumy ta zauna a gidan amma tayi alkawarin making life dinta miserable.

Zee sai murna take, dan batama yi expecting samun wani abu ba, tunanin ta daya shine Wacece sumy ya take, itadai tasan sumy diyar alhaji da mommy ce amma bata taba ganinta ba.

*Bayan shekara daya*

Sun gama exams sai shirye shiryen tafiya suke, kursum dake wasa da hanifa tace sis yanxu kina ganin idan nabi ki gidanku ba matsala , nidai ina tsoro kar hajiya tamin wulakanci ta kore ni, dan yanda kike ban labarin halinta na rashin kirki nasan tana iya wa.
Sumy tace karki damu nasan yanxu ta canza tunda shekaru sun ja, kuma makauniya ce ba lailai bane tasan kina gidan ba......

An turo driver daga gida daukan su, sai sallama suke da kawayen su da sauran malaman makaranta , suka shiga har office din gimbiya hafsatu sukai mata sallama  ta dauko wani dan karamin box ta bude taciro wani hadadden pink diamond da take ajiye dashi wajen shekaru goma sha takwas da suka wuce ta damka wa kursum a hannu, tace yaudai na cika alkawarin, kursum tace wanna na miye kuma, gimbiya tace matar data kowa kine tun kina jiririya tace in baki idan kin tashi tafiya kya iya siyarwa ki samu na rike kanki,
Kursum tai mata godiya sosai suka fice, sun iske driver na jiran su,  suka shiga mota...
koda suka shigo cikin gari sun tsaya suka shiga gidan Inna sadiya (mai kitson su) suka gaishe ta sosai ta amsa da fara'arta dama tasan da zuwan su, sumy ta mika mata hanifa, Inna ta amshe ta sai wasa take mata tace karku damu zan rike muku ita har kudawo daukan ta dama nagaji da xaman kadaice. .....
Kursum tace Inna mungode sosai, da munyi settling zamu zo mu dauke ta yanxu ki rubuta mana number wayan ki yadda idan mun isa gida zamu kira, dan yanxu ba waya ahannun mu, "Suka bata kudi masu yawa wanda zai ishe su kafin su dawo, suka kama hanya sai kanon dabo...
amota sumy sai kukan rabuwa take da hanifa, tabbas tasan barin hanifa wajan Inna shine daidai dan tasan hajiya bazata taba yadda da cewan tayi aure harta haihuwa ba, shiyasa ma tabar ta hannun Inna kafin tasamu yi mata bayani. ......
Sun shigo kano kenan, sumy tace gaskia yaka mata kindan gyara fuskan ki kodan kwalli ne kisa a ido, kursum tace kinsan ni bana kwalliya asalima ko kayan kwalliya ban dashi, sumy ta mika mata handbag dinta tace bude kidau powder ki sha fa,
Daidai lokacin da kursum ta amshi jakar sumy wata katuwar motar petur dake tafe ta bangaje motar su, kofan side din da kursum ke zauna ya Bude ta fado kan titi  rike da jakar sumy, sai birgema take harta buge da wani katon dutse, sumy da driver kam suna cikin mota dake kamawa da wuta sai gangarawa motar take cikin daji harta bugu da wani katon bishiya tayi exploding baammm kawai kake ji. ...

😳😳😳😳

       *Xarah Bêê*

*Dedicated to Bady social*
     
        ~Luv u all~😘😘😘

No comments:

Post a Comment