[04/10 6:12 AM] 💕: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺
🌺🌺 by ~Xarah Bêê
Page 1⃣ ~ 5⃣✨
Sauko wanshi kenan daga jirgin sama,daka ganshi kaga dan hutu ne,dago ne fari kakkyawan gaske,ga dara daran sexy eyes dinshi..........driver yaxo airport ya dauke shi sai cikin garin bauchi,har hotel din daya sauka driver ya kaishi....
Bayan awanni kalilan harya shirya cikin kanana kaya masu kara fito da ainuhin kyawun shi,ya kira abokinshi huzaifa dan ya yadan zaga dashi yaga gari, sun gama zagawa suka biya wani eatery dan cin abinci......
Tafe suke suna dan hira,kursum na cewa kawarta itafah ta gaji da wannan wahala su kenan kullum yan Aike suka zama, sauran dalibai na hostel amma su suna nan suna supervising kayan abincin makaranta har sai an shigar da komai kitchen,Sumy tace haba kursum miye aciki toh ai aikin lada ne kuma koba komai ai mun ga gari..............kursum taja tsaki tace to ai sai kije ke kadai saboda ni xan dan leka gurin masu wasa da monkeys (biri).
Sumy tayi kwafa ta wuce abunda inda sabo ai ta saba da halin aminiyarta........
Kursum kenan,yarinyar yar kimani shekara sha bakwai a duniya,ga kyau, sam batason hayaniya, amma idan ka tabo ta sai inda karfin ta ya kare
Wannan kenan....
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[04/10 6:12 AM] 💕: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
🌺🌺 By ~Xarah Bêê
Page 6⃣~ 1⃣0⃣✨
Gaskia garin nan fah akwai mata hadaddu, ya kamata ace kafin in bar garin nasamu babe (yarinya) wanda xan huta da ita, huzaifa yaja tsaki ya kalle shi kaidai yazid kana nan da halinka na playing mata bansan randa zaka natsu ba, Ina fatan Allah yakawo wacce za tayi maganin ka..........Yazid yace aini babu macen data isa tayi magani na, asali ma ban dauki su abakin komai ba face rigar canxa wa👕👔
Sumy ta gama aikin da take ta biya eatery cin abinci, shiganta kenan tayi ido hudu dashi, wow ta fada cikin xuciyan ta gaskia kiya guy dinnan is hot ya hadu iya haduwa....😍😍😍
bata ida xancen xuci ba kawai taji ya mata sallama ai ba shiri ta saita kanta ta amsa ta gaishe shi, da fara'arsa yace mata ni sunana habib acewar yazid Ina fatan baza kimin rowar sunanki ba...
tayi murmushi tace sumayya suna na yace nice name sumy Ina kike xama ne naganki da school uniform, tace aikina director dinmu yayi school din bayan wajen nan yake ma, yace okay nagane skull din.
Yayi murmushin mugunta yace naga kinmin ne gashi you are so quite Ina fatan dai xaki amsa min tayina, sumy ta sunne kai xuciyan ta fal da farin ciki, yau dai ta samu prince charming din da take mafarki........
yazid ya dauko wani hadadden xoben azurfa💍 mai shegen kyau da tsada ya zurawa mata a hannunta amatsayin son dayake mata sumy tayi godiya tace zata wuce dare ya farayi yace yaushe xamu sake haduwa, tace ko xuwa gobe muna iya haduwa anan yace toh Allah kaimu ta wuce. .......
yayi murmushi mugunta da alaman yarinyan bata da wayo, tabbas zan samu abunda nake sha"awa tattare da ita..ya wuce waje wajan abokin kinshi daya cika yayi fam dan jiran ya dawo su wuce huzaifa yace Allah ya shirye ka yace Amin suka wuce.......🚗
Ina Kursum take ne?
Waye yazid ?
Wace kuma sumy ?
Mai yakai kursum da sumy makarantar boarding
wanda babu marabarta da gidan marayu ?
Ku buyoni dan jin asalin labarin
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[04/10 6:12 AM] 💕: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
🌺🌺 By ~Xarah Bêê
Page 1⃣1⃣~ 1⃣5⃣✨
Har kusan yamma sannan ta dawo, ta tadda sumy kwance sai faman murmushi take tana lumshe idon ta kursum ta daka mata duka tace lafiya ki kike wani murmushi kaman wata charisma goat (akuyar krisimeti) ko dai baba ne ya shigo gari, sumy tace kedai yau nayi new catch fah guy din ya hadu iya haduwa ba karya, wani irin so da kaunan shi ke ratsamin zuciya...........
Kursum ta yatsane fuska taja tsaki, kedai raba kanki da soyayya tun yanxu saboda maza basu da tabbas kila ma dan iska ne, sumy tace haba banda habib dina dan kuwa nasan yana sona, munyi dashi ma xamu hadu gobe dan Allah kursum ki taimaka ki rakani gobe kinji my cwt sis😔
Yazid kwance a tafkeken dakin hotel din daya sauka da alama waya yake, yace haba xee kiyi hakuri mana nace makin nan na 4days xan dawo duk kin dakamin hankali....xee tace haba ya yazid tun jiya fa yakamata ace ka dawo wlh nayi missing dinka sosai gaba daya garin kano yamin zafi, jiya har wajen ummanka naje na mata wuni ko zan kanga amma shiru kuma gashi wayoyin ka duka akashe.....kiyi hakuri my love zan dawo dana gama aikin dana ke abubuwa sun min yawa ne, tace to amma dai kayi promising nan da 4days ko yace eh ya kashe wayan......xee rigiman ki yayi yawa wlh amma dole in koma saboda dad bai san bana gida ba.
Makaranta ce babba nagani nafada mai tsadar gaske wanda sai dan wane da wane, ita ba gidan marayuwa ba kuma bawai makaranta jeka ka dawo bane ko boarding, yawan ci student (dalibai) din dake makarantar iyayensu basu da lokacin kula dasu, tun yara na kanana ake kai su har sai sun gama senior year sunkai 18 years old (shekaru goma sha takwas) Sannan iyayen su ke zuwa daukan su.......Gimbiya Hafsatu itace director din makarantar gata da zalama dason abun duniya,babu ruwanta idan kakai 18years iyayenka basu zo daukan kaba saita aurar dake acewarta iyayenka sun manta dakai ne......
Yau ta kama weekend fito wansu kenan daga hostel zasu shiga gari, daka gansu kaga aminan juna👭....kursum tace kin tabbata saurayin nan naki zai zo, ina fatan dai ba jirga ki zai yiba sumy tayi dariya tace haba dai aini na yadda dashi dari bisa dari, maybe ma yana can yana jirana ma
Sun iso wajen haduwan kenan sumy tace wayyo na manta da xoban daya bani jiya akan gado kuma gashi namai alkawarin bazan cire shi ba dan Allah kursum kiyi hakuri ki jirani anan barin koma hostel in dauko.
Kursum ta wurga mata harara, tace kedai wallahi baki da wayo sam, dan wahala shine xaki koma ki dauko toh ai sai kije ni ina nan idan kuma kin dade in kara gaba abuna, "sumy tayi murmushi ta bar wajen da sauri ta.
Tana nan tsaye har kusan minti goma, taji wani lausassan murya yana mata sallama ta juyo sukai 4 eyes saida numfashin ta ya kusa dauke wa saboda ya hadu iya haduwa, ya sakan mata wani irin yaudararen murmushi, ta hade rai tace malam nasan kane, yazid yace a'a baki sanni ba, asalima ni bako ne yau Nashigo garin suna na kabir yana murmushi yana shirin jawota jikin shi, ai bai ankara ba ta wanke shi da mari an gayama ni yar iska ce, waye ma kai dahar xaka naimi tabani.........kallon ta kawai yake yana shirin magana sumy ta iso wajen fuska a murtuke tana tambaya meke faruwa taja kursum gefe tace shine saurayin nawa fa naga kina shirin yimai rashin mutunci kursum tace sis ki raba kanki da guy dinnan kabir ban yadda dashi ba da alama yana da wani hidden agenda tattare dashi.
Sumy ta daure fuska tana mata kallon bakida hankali wato bakin ciki kike min danke baki da saurayi toh baki isa ki rabani dashi ba yanxu nafara sonshi kuma harda aure xamuyi, sunan shi habib not kabir tayi tsaki ta bar kursum nan tsaye da mamaki.
Yazid yace amma kawarki bata da mutunci tana ganina tafara zagina, sumy tace dan Allah kayi hakuri kar kayi fushi bata sanka bane, yace to ya wuce ya kike me zan samu ne yana magana yana rike da hannunta yana lashe lips dinsa sai lumshe ido yake, tace lafiya kalau nake" anan garin kake zama ne yace eh ai gidanmu bai da nisa daga nan, iyayena sun rasu, wajen kawuna nake tun ina karami tace wayyo Allah yaji kansu da rahma ta tausayamai sosai wani irin sonshi ke kara shiga zuciyar ta.....
Ni yanxu bani da kowa sai kawuna sai kuma ke, "ya kara janyo ta jikinshi yaxe plz sumy karki kujeni I love you with all my heart, xaki aureni ? "Ba shiri sumy tace eh kaman dama jira take ( I pity u sumy) , yace to yanxu ya zaai Kince parent dinki suna kano kuma ni inaso in mallake ki amatsayin mata ta, tace babu damuwa babana sau daya yake zuwan min visting a shekara kuma yana sona sosai idan yaga na auri wanda nakeso shima zai ji dadi, yanxu kawai director din makarantar mu Gimbiya Hafsatu xaka samu sai kuyi magana saika turo a naimi auran ko gobe kakeso ana iya daurawa.....
Shi kam sai kallonta yake azuciyan shi yace lailai yarinyan nan bata da wayo ko kadan, burina kawai in samu abunda nasamu in tattara in gudu bazama ta kara gani na ba.
Yazid yace kina ganin babu matsala danni acikin kwana uku nakeso ayi auren dan baxan iya rayuwa bake ba, tace babu matsala gimbiya Hafsatu tasan abunda ya kamata...ya rakota har gaban makarantar sannan sukayi sallama ta wuce ciki shima ya tafi yana farin cikin da baisan na miye ba.
Hmmmm
Muje xuwa dan jin cigaban labarin
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[04/10 6:12 AM] 💕: 🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
🌺🌺 By ~Xarah Bêê
Page 2⃣1⃣ ~ 2⃣5⃣✨
Haba sumy yanzu da bakinki kika aminci da auran stranger din da baki ma san halinsa ba, ko aure baki sani ba balle iya zama da miji asalima ma ko dadewa bakuyi da haduwa ba......
Dan Allah kursum ki kwantar da hankalinki kema kinsan banda wani option daya wuce in aure shi tunda har muna son junan mu, kuma nidai akan in koma gurin momy da zama na gwamma ce in auri stranger dinnan cause hankalina yafi kwanciya dashi I don't want to lose wannan opportunity din dana samu, kursum tace to mai zaki cewa daddy kinsan nan da wata biyu zaizo ganinki, tace dad ba matsala bane, na tabbata sai yafi kowa murna da auran nan.
Kursum tace toh Allah yasa hakan yafi alkhairi, duk jikinta yayi sanyi ranta abace ta rasa dalili,😔😔😔 tana ganin dan zata rabu da aminiyar ne shine yasa ta jin hakan.
****************************
A yau ne aka shaida daurin auran yazid (habib) da sumy, babu wani event da akayi illa abinci da gimbaya hafsatu ta bada a dafa, anci an koshi jama'a sun watse kafin dare kuma akai amarya 💃🏿💃🏿💃🏿
Ango kam sai washe baki yake, 😀😀😀 babu wani aboki ko dan'uwa dayasan da batun auran face kawu jamilu daya tsaya mai akai komai cikin kwanciya hankali...
Ko huzaifa abokinshi bai san abunda. Ke faruwa ba, dan yasan idan ya gayamai plans dinshi xai ruguje kenan, asalima yamai karyan ya koma kano.
Amarya sumy sai shiri take tana hada kayanta cikin akwati, farin ciki fal fuskan ta, lokaci kawai take jira akaita gurin heart beat dinta. 💃🏿💃🏿💃🏿
Ta kalli kursum data takure karshen gado, daka ganta kasan tana cikin tashin hankali....tace haba sis muna nan tare fa bawai guduwa xanyi in bar kiba, kursum tace dole hankalina ya tashi bani da kowa sai ke sumy, idan kin tafi maraicina zai dawo sabo ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sumy ma tana kuka tazo ta rugumeta tana kara bata baki akan tayi hakuri suna nan tare, mutuwa ce kadai xata iya raba su. 😭😭😭
Da daddare kawu jamilu da kanshi yazo dauka amarya, gimbiya hafsatu da kursum kadai suka mata rakiya har gidan mijinta,
Gida ne dan karami, mai dauke da room & parlour sai kitchen daga gefe sai dan karamin tsakar gida, cikin dakin kuwa babu wani abun kirki aciki sai kafifa kawai da stool na zama, dama baa jera mata komai ba tana jiran idan daddy ya zo sai ya siya mata komai da komai.
Gimbiya hafsatu da kursum sun mata nasiha sosai, sanna suka mata saida safe suka wuce abunsu.
Kamshin turaren sane yasa tagane yashigo dakin, yaxo ya xauna kusa da ita ya jawo hannuta ya sumbata yana kare mata kallo, yarinyar so innocent..........
Sakonnin soyayya ya aika mata a darenan da kyau,masu rikitarwa, har ya samu biyan bukatan shi, saida yaji kukanta na yawa sanan ya dan saurara mata......
Koda ta farka da safe baya cikin dakin, dakyar ta tashi ta shiga toilet ta tsarkake kanta tayi wanka ta fito tayi sallah harta koma bacci, sai wajen 10am ta tashi, tayi mamanki still baya na,ta tashi ta leka ko ina a gidan amma bayanan kuma babu alamunsa......
Ta koma daki dan duba kayan sa, nan ma wayam tagani sai wata wasika daya ajiye mata kamar haka
Matata mai sona, Allah yayi miki albarka kin biyani ni arayuwa.......amma dan Allah ina naiman gafararki da ki yafemin dan bawai na aureki dan ina sonki bane face sha'awarki danayi, kuma ni bazan iya zina ba shiyasa na aureki, amma kiyi hakuri sumy, na sakeki saki biyu sannan ga kudade masu yawa nabar miki ki kula da kanki, karma kice xaki naime ni dan kuwa baxa ki taba ganina ba. Sannan kina iya zama acikin gidan na wata daya kafin kudin hayan ya kare..............ina miki fatan alheri.
Bissalam
Innalillahi wa inna'ilaihi rajun kawai take fadi, ta fadi kasa tana rusa uban kuka shi kenan taga ta kanta
kursum ce ta shigo gidan da abincin karin su, ba karamin girgiza tayi ba da taga kawarta cikin yanayin nan tace miya faru? Kukan mai kike yi? baki da lafiya ne, a gigice take jero mata tambayo yi......... sumy kam kasa cewa komai tayi, ta mika mata wasikar daya ajiye mata, kursum ta girgiza matuka data karanta kasa cewa komai tayi, itama ta zauna sai kukan suke babu mai rarrashin wani. 😭😭 kaico
Daga bisani suka tashi suka dau kayan sumy da makudan kudin daya bari suka bar gidan.....
Yazid kuwa tunda ya tashi yawuce Airport yana sauri baya son missing flight dinshi na 7am, Allah yasa yana xuwa dama shi kawai ake jira, jirgi ya daka sai kanon dabo.......
Umma ce da kanta taje dauko shi a airport, dan kawai yasan ta damu dashi, suna cikin mota umma tace, son wato ka gujemu ko, wajan wata daya kenan bansa ka a ido ba idan nakira wayan ka saika ga daman dauka......
Yace to umma ya kikeso inyi, keda kika fi bawa aikin ki (fashion designer ce) mahimmanci, ko a gida baki da lokacin kowa saina aikin ki, ki wuni kina aiki a office kuma ki dawo gida kinayi, har Abba ma yafiki samun lokaci na, "tace my son kamin uzuri dan Allah, aikin nawa ne dole saida attention sosai in ba haka ba komai bazai yi daidai ba, ni kaina inason kasance wa da family dina shiyasa ma nakeson daukan hutu kona wata biyu ne......yace toh shikenan umma duk yadda kikai yayi daidai, shidai arayuwan shi yanason ummansa bai hadata da komai.
Koda gimbiya hafsatu ta karanta wasikar sumy, sai cewa tayi karta damu dama maza basu da tabbas, itama tayi mamaki yadda yayi ta zubar da kudi kaman bai san ciwon suba, indai aure takeso zata iya naima mata wani ta aura kodan ta huce haushi.
Kursum tace haba gimbiya kamata ace kin naimo mijin nata ayi magana,tunda da hadin bakinki akayi auren nan kuma ai kinsan kawunsa, gimbiya tace tab aini yanxu ko nayi trying number kawun bai shiga kashe wayar take
kuma yarinyan ita da kanta ta nuna shi take so kuma xata aure shi, toh miye laifina aciki.......ki fice min yanxu nan marar kunya, wato kece da bakin magana ita da aka saka bata zoba sai ke, wawiyar banza.
Kursum ta fice ranta abace,bata taba ganin zalamar miyar mata irin gimbiya ba, ita dai kanta kawai tasani......
Ta koma dakinsu, har lokacin sumy kuka take duk ta rame ta fita hayyacinta lokaci daya, kursum tace mata dan Allah ki bar kukan nan haka, indai ina raye a duniya toh saina naimo shi na daukar miki fansar abunda ya miki, koda kuwa zaiyi causing life dina, dat is a promise, sau daya nataba ganinshi amma bazan taba mantawa da face dinshi ba......
Tana taba sumy baki hardai ta hakura ta barwa Allah komai..
*Bayan wata biyu*
Sumy sai rashin lafiya take ga zazzabi da weakness da take ji ga yawan amai , shiyasa gimbiya ta kaita asibiti, doctor ya mata gwaje gwaje ya gano tana dauke da cikin wata biyu.......aka sallamo su suka dawo.
Gimbiya ta kirawo kursum ta gayamata sumy na dauke da cikin wata biyu, sai data girgiza da jin wannan xancen, yanxu ya sumy zatayi idan tasan tana dauke da cikin wanda yama manta da zamanta, gimbiya tace ga test result din saiki bata ki kara kwantar mata da hankali, kinsan mai karamin ciki batason tashin hankali gudun kar ciki ya zube.
Ta karba sum - sum ta fice, tasamu sumy na karatun al-qur'ani, sai da tajira ta idar sannan ta mika mata test result din, sumy ta karba ta duba saida gabanta ya fadi tace wake dauke da ciki ? Kece kowa?
Kursum tace kinsan dan Adam ajizine, duk yadda ubangiji ya tsara aka ke faruwa babu wanda ya isa yaja da ikon Allah, komai na duniyan nan jarabawa ce, Dan Allah kiyi hakuri ki yarda da kaddaran da Allah ya daura miki, sumy tace meke faruwa ne ? kinsani a duhu fah.
Ciki gareki na wata biyu sumy, kece keda cikin ba kowa ba, hawaye kawai sumy take tana addu'an Allah yasa hakan yafi alheri agareta, kursum tace amin.
Daddy ne ke tuki hankali kwance, yana murnan yau zai ga diyar shi tilo a duniya, wajen shekara guda rabon daya ganta..
Ya iso makaranta, har visitors lodge (inda iyaye ke zama idan sunzo ganin ya'yan su) aka kaishi, aka tura kiran sumy tazo dad dinta yaxo.....ita da kursum suka je wajen daddy suka gaishe shi, gaban dad sai da yafadi ganin yadda sumy ta rame sai haske data kara sosai, yace kursum, sumy bata da lafiya ne? Kursum tayi shiru ita dai tarasa dalilin daya sa idan tana gaban baban sumy take jin wani iri, kaman akwai wani connection tsakanin ta dashi.........kukan sumy ne yadawo da ita daga tunanin da take, tana kuka tana ba daddy labarin abunda ya faru tun daga auran ta har izuwa yanxu da take dauke da ciki, daddy kasa magana yayi sai hawaye kawai, gaskia ya tausayawa sumy ba kadan ba, duk laifin hajiya hadiza ne, da yanxu sumy na gida agabanshi hankalinta kwance.
Yana taba sumy hakuri akan karta damu jarabawa ce ta ubangiji, komin wuya akwai dadi, ya ajiye masu shopping din daya masu sa'annan ya masu sallama zai koma kano, karshen shekara zai dawo ya dauketa, ya dauko makudan kudi yabasu suna ta godiya..
Daddy kam yayi niyyan kwana biyu, amma bazai iya jure ganin sumy halin da take ciki ba, shi kanshi daurewa kawai yake amma ranshi a bace yake, aka ya tattara ya koma kano,
Hajiya hadiza na hakimce a parlour a zaune tana jiran shigowan daddy gidan, dan ta kwarara mai buhun bala'in data saba akan yaje ganin yar tsintuwo bada izinin taba....
Yana shigowa ta gane muryanshi da sallaman da yayi bata ma damu da yanayin shi ba, ta hau zaginshi damai rashin kunya ta ko ina, daddy kam kasa magana yayi ma saboda bakin ciki ta riga tamai yawa, nan take shikam ya yanki jiki ya fadi sai jin faduwan mutum tayi tim akasa.....😳😳
Ta kwallawa samira (yar aiki) kira maza ta fito Alhaji ba lafiya, samira ta fito da gudunta tana hajiya, alhaji ne ya fadi da alama ma rai yayi halinsa.
Hajiya a rude tace "samira kiramin wayar shehu nasan baiyi nisa ba,kirashi mukai alhaji asibiti.....
Baba shehu da sauri ya iso gida,suka sa alhaji a mota sai asibiti
likitoci sun yi iya kokarinsu, amma rai yayi halinsa (kulli nafsin za'ikatul mauti), abun tausayi hajiya da baba shehu sai kuka suke yau sunyi babban rashi.
Doctor yasamu baba shehu da hajiya ya tambaya su ya akayi suka bari har zuciyan alhaji ya buga alhalin sunsan yana da ciwon zuciya, hajiya tayi tsuru tsuru bata ce komai ba illa kukan da take tayi dan tasan tabbas itace silan ciwon zuciyan alhaji, yanxu gashi ya tafi ya barta, kuka kawai take tana nadaman abunbuwa data shuka mai........
Nima kasa rubutu nayi saboda mutuwan daddy ba karamin girgizani yayi ba...... Rip😭😭😭
*Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘😘
No comments:
Post a Comment