🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺
🌺🌺 by ~ Xarah Bêê
page 5⃣1⃣✨
Abincin ma kasa Ci tayi dan haushi, ta fito zata wuce dakinta zee ta finciko ta, tace ke yar titi ki fita daga ido na, ke har kina da bakin Kiran mutum dan iska, wayasan iskanci da kikayi a makarantar da aka jefar dake, ina baki last warning ki fita daga rayuwa ta......
kursum bata ce mata komai ba illa gyara rigarta da tayi ta wuce abunta, zee tayi kwafa tace lailai ma yarinyan nan, ya zama dole in binciki past dinta, xanje har makarantar da aka riketa in samu wani abu akan rayuwarta. ...
umma ce zaune a daki tana duba new designs dinta a laptop, yayi sallama ya karaso ya fada kan gado, tace my son daga ina haka a darennan, naga ma ranka abace, hop all is well ?
yace ba komai dama wajan zee naje, nan take umma ta bata rai, ita dai bata kaunar zee ko kadan, dan farin cikin son dinta take nuna tana sonsu tare, ya nisa yace umma dama hajiya hadiza nada ya' budurwa ??
Dam gaban umma yafadi dan tasan tabbas hadiza nada diya kuma yanxu ta zama budurwa, tace my son hajiya bata da diya tun wajan haihuwa yar'ta ta rasu, nasan dai alhaji yayi adopting yar yarinyar daga gidan marayu, zaman su yaki dadi da hajiya shine yakai ta wani boarding skull....
yazid yace ta dawo ai, ita nagani a gidan dazu, yarinyar sai rashin kunya da raina mutane, umma tayi dariya tace haba son daga ganin yarinya sai aibata ta, Allah umma dagaske nake sau biyu muna haduwa tana min fitsara, sam bana sonta😕😕
umma dai dariya kawai take yadda ya dage shi baya sonta, sai kace ance ya so ta, tace son abbanka ya wuce England dazu, yayi trying line dinka switch off,
yace eh wlh I was so busy ne, zan kira shi gobe, tace to yace dai karka manta gobe ka kai ayi signing document din daya baka dazu,
yace toh umma barin je in kwanta good nyt, okay nyt my son.
********
sauri take ta wuce office dan yau ta makara kuma suna da meeting, harta fito daga daki ta kara komawa da sauri, ta bude side drawer ta dauko pink diamond dinta, tayi murmushi, ta san koba komai tana da abunda uwarta ta ajiye mata,
ta saka pink diamond din jikin chain din wuyanta, ta fito tayi kicibis da hajiya abakin kofa amakale
tace hajiya ina kwana, mai kikeyi abakin kofana ? kina son wani abune ?? lokaci guda take jero mata tambayoyi, hajiya data gigice ganin diamond din wuyanta yasata fara kame kame, tace daban kwana ba zaki ganin, shegiyar yarinya toh wuce wa xanyi ta wuce fuuuu har tana naiman faduwa, kursum dake tsaye tana mamakin hajiya, anya matan nan bata gani kuwa, ta rufo dakin ta wuce.
hajiya ce a daki sai sake sake take da tunani iri iri, ina yarinyar nan tasamu diamond din nan, nasan ni kadai keda irinshi kuma na bayar dashi dadewa, wayarta ta dauko tayi dialling line din mairo dan tasan ita kadai ce zata bata amsar komai, ringing daya umma ta dauka, kafin ma su gaisa hajiya tace mairo kizo gida inason ganinki, ina son muyi magana akan abunda ya faru shekara goma sha takwas da suka wuce......
Dam gaban umma ya fadi, 😳😳😳dama tasan zaa rina.
🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺
🌺🌺 by ~ Xarah Bêê
page 5⃣2⃣✨
Tana isa boardroom ta wuce, "suka fara meeting, dama ita kawai ake jira, "baba shehu sai zuba bayani yake, ita dai bata gane komai ba har aka gama, ta koma office dinta.
baba shehu ne yashigo office din, sai wani fara'a yake kaman dagaske, "kursum tace baba da kanka, ayda ka turo wani, yace "nida ya'ta ai dole inzo gaisheki da kaina, ya mika mata check din makudan kudi tayi signing, ta karba ta duba tace "baba kudin sunyi yawa, me xaai dasu ? "ya sosa keya yace dama wasu sabbin machines na company mukeso importing dan wanda muke dasu sun fara lalace wa. tace toh shikenan amma dai xan rage kudin sunyi yawa, tayi signing ta mika mai, bai ji dadin abunda tayi ba ya amsa ya fice rai abace, ita dai kursum bata yadda da fara'arsa ba kwanan nan sabanin da idan ta gaishe shi sai harara da zargi yake wurgo mata.
zaune yake a office yana duba takardun dake gabanshi, can ya hango papers din shares dinsu da abba ya bashi yakai T. b oil & investment company asa hannu, da sauri ya mike ya kwashe papers din tare da car keys dinshi ya fice🏃🏼🏃🏼
Da sauri yake driving har ya iso company din, ya tambayi daya daga cikin workers din inda office din MD yake, suka kai shi office din Mr dabo, da sauri mr dabo ya tashi ya gaishe shi dan yasan family dinsu ne major share holders din company din, "Yazid ya bashi hannu suka gaisa dan ya sanshi sosai mutumun abba ne, "yace mr dabo ashe kaine new MD din, dabo yayi dariya yace ai bankai matsayin nan ba, nine dai personal assistant din new MD din, barin gayamata tayi bako, da sauri ya fice ya dawo yace kana iya ganinta yanxu, "Yazid yace okay thanks.....
Hankalin ta kwance sai buga game take abunta, yayi knocking kofa, ko dagowa batayi ba tace come in, yana karaso ciki ya ganta yaji mugun takaici, dama witch dinnan itace MD din, lailai ko yau idan tamai fitsara bazai barta ba, bai ankara ba yaji tace can I help you ? ya kara kallonta wato ko dagowa baza tai ba game dinta kawai take, lailai ko zanyi maganinta. ......
Papers din hannun sa ya watso mata a fuska, da sauri ta dago suka ido, sai da gabanta ya fadi dan ba karamin kwarjini ya mata ba, ta harare shi, ta daure tace "miye haka zaka watso min papers, have u lost your manners ?
ya bata rai, "yace aiki kika zoyi ko game, ko an gayamiki wasan yara ake anan, ta murguda baki tace "bansani ba ina ruwanka, dariya ma ta bashi, yace "signing zakiyi akan papers din" ta yamutsa fuska tace na miye , harara ya wurga mata yace baki iya karatu bane, "ta hada papers din waje daya ta karanta ta kalle shi tace "ashe kuna da shares a company dina" yayi banza da ita , tayi murmushi ta tashi ta karaso gaban shi ta ajiye mai papers din tace " banda pen ( biro) balle inyi signing, kana iya komawa da papers din, next time idan xaka zo saika hado da pen ✍🏻✍🏻
ta zauna taci gaba da game dinta...
Bai ji haushi abunda tace ba, ya tashi yadau papers din yai murmushi ya kalle ta yace" I have nothing to say amma keda kanki zaki ne me papers din, ya fice daga office din.
Mr dabo ne yashigo office din da saurin sa yace madam lafiya dai koh, naga bakonki ya fita a fusace, ta yatsine fuska ta gayamai abunda ya faru, yace "madam ai kinyi kuskure babban saboda sune major share holders din company dinnan, idan suka kwashe shares dinsu company dinnan zai zama bankrupt kuma zaiyi affecting oda share holders, "kursum da hankalinta ya tashi tace mr dabo yanxu ya xaai kenan dan papers din na hannu shi, "yace abu mai sauki tashi zakiyi muje har office dinshi ki bashi hakuri ya baki papers din, "tace to muje " handbag dinta ta dauka da sauri suka fice...
umma ce ta shigo parlour gidan da sallaman ta, shiru babu wanda ya amsa "can ta hango zee zaune tana kallon tv da alama batasan ma ta shigo ba, ta karasa ciki tace baki ji ina sallama bane , ta juyo ta kalle ta aya tsine tace banji bane sorry, umma tare kuke da yaya yazid ?
umma tayi banza da tambayan tace ina hajiya ? zee tace bansani ba amma ki dubata sama, ta cigaba da kallon tv abunta. .....Umma tayi kwafa ta haura sama, tana takaicin hali irin na zee, sam batayi sa'ar suruka ba.
hajiya ce zaune a daki sai kuka take tana dana sanin jefar da yar'ta datayi, babban tashin hankalinta shine rashin gayawa daddy cewan yar'su bata mutu ba harya rasu, kuka kawai take tana dana sanin bakin halin data shuka a rayuwarta, "da sauri umma ta karaso wajanta tana hadiza lafiya, meke damunki ? hajiya tayi shiru tana tunanin yadda zata gayawa umma ta ga pink diamond dinta awuyan sumy, saboda kowa yasan makauniya ce, ta nisa tace "shekarun baya da suka wuce nayi niyyan jefar da ya'ta, amma kika dauketa kika kaita inda zaa raineta harta girma, "ta kara fashewa da kuka tace mairo ina ya'ta kursum take ? kina da labarinta kuwa ??
umma ta gyara zama tace "hadiza ni bansan inda yarki take ba, makarantar dana kaita munyi dasu idan takai shekara sha takwas zasu sallameta, kuma yanxu ko ta cika sha takwas dan gimbiyar makarantar ta kirani ta gayamin tacika alkawarin dake kanta na bawa yarinyar diamond din da kika ajiye mata. ...
agigice hajiya ta kalle ta, tace mairo ki taimakeni ki kiramin gimbiyar awaya, ko zata San inda ya'ta taje ranar da suka sallameta, umma tace to barin kirata muje, dan nima tunda nakai yarki makarantar ban yanke zumunci da gimbiyar ba, dan nasan wataran zaki nima yarki.....
Tasa masu call din a speaker, ringing daya biyu Gimbaya hafsatu ta dauka da fara'arta, suka gaisa da umma, "umma tace dama zancen kursum ne, ko kina da labarin inda take yanxu, gimbiya ta nisa tace "ai kursum Allah yayi mata rasuwa tun lokacin da muka sallame ta, kawarta tabi suje gidansu a kano shine sukayi hatsari a hanya, ita ta rasu amma kawar bata rasuba, "Dam gaban hajiya ya fadi, shikenan yar'ta ta rasu" umma tace gimbaya ya sunan kawarta ? tace sumayya tanimu bawa sunan ta, umma tace nagode sosai gimbiya sukai sallama.
Rudani, tashin hankali, lokaci guda hajiya ta shige su, ta kalli umma da jajayan idonta da suka rine tsaban kuka tace "babu tantama sumayya gidan nan ce kawarta, tare sukayi accident kursum ta rasu, kuka kawai take tana salati , taga samu taga rashi, "umma sai bata baki take tana kwantar mata da hankali, amma ina kuka take , bata ankara ba sai gani tayi hajiya ta fadi kasa sumammiya.
😳😳😳😳😳😳
🌺🌺🌺 Kursum 🌺🌺
🌺🌺 by ~ Xarah Bêê
page 5⃣3⃣✨
Umma ta tashi ta dibo ruwa ta yayyafa mata, amma shiru hajiya bata tashi ba, a gigice ta fito ta kwalla wa zee kira, zee tazo da saurinta tana "umma lafiya kuwa?? tace ba lafiya ba maza kira doctor malik, hajiya ba lafiya, "da sauri zee tayi kiran layin doctor tana gayamai abunda ya faru, "doctor yace ni yanxu am very bixy , zan turo ambulance yanxu akawo ta asibiti, "zee tace toh dr. muna jira.
Ba'a fi minti biyar ba, ambulance yazo suka wuce asibiti gaba daya, direct emergency aka wuce da ita, umma da zee na daga waje hankalinsu duk atashe, umma tace zainab kin gayawa shehu muna asibiti kuwa? , tace eh yanxu na kira shi yana hanya zuwa ma, "umma tace tun dazu nake trying line din yazid ban samu ba, gwada kira min shi ko zaki samu, "zee tace nima dai tun dazu nake trying line dinshi ban samu ba, amma barin je office dinshi inji ko lafiya, umma tace toh ki gayamai ina naiman sa yanxu nan, tace to ta wuce.
Zaune yake a office yana sipping coffee, yana danna laptop dinshi hankali kwance, ya dauka papers din ya kare masu kallon, yayi murmushi ya ejiye su gefe, secretary dinshi suzzie ta shigo, "tace sir a lady is here to see you, "yace owkay tell her to come in" suzzie ta fita tace madam u can go in, kursum tace tnx, ta juyo ta kalli Mr dabo "tace karna batama lokaci, kana iya komawa office, idan nagama zan naimi taxi indawo, yace toh madam sai kinzo, ya wuce.
Ta turo kofan tashigo, wani irin kamshi mai dadi da sanyi suka mamaye ta, offfice din mai girman gaske dan har yamafi nata, dago wa yayi ya kalleta yayi murmushi ya cigaba da abunda yakeyi, "ta karaso tace mai sannu taja kujera zata zauna, ya dakatar da ita yace "baa zaman min a kujera saida izini ni na, kuma miya kawo ki nan?? Tayi shiru ta koma gefe ta tsaya, "tace humm mm dama papers dinnan zaka bani inyi signing" yayi banza da ita kaman beji abunda tace ba. Har kusan minti biyar baice komai ba kuma bataga alaman zaice ba, ga tsayuwar ta isheta daurewa kawai take, "kashe laptop din yayi ya tashi ya dibi wasu files, ya kalleta yace kina iya zaman a couch din can kiyi game din da kikasaba, ni yanxu ina da important meeting da zanyi attending" bai jira abunda zata ceba ya fice.
Ba yadda ta iya dole ta jira shi, ta bude jakanta ta dauko wayanta ta fara game, har kusan 30mins bai dawo ba, gashi ta gaji da game din, ta kwanta ta fara bacci abunta, "bayan awa daya ya shigo ya cigaba da aikin gaban shi, yama manta da wata a office din, can ya dago zai dauki wasu files ya hango ta kwance kan couch tana bacci da alama ma sanyi Ac yamata yawa dukta takure waje daya, ya dauki papers din ya taso zuwa wajenta da niyyan ya tashe ta, ya tsugunno setin fuskan ta yana kallonta, yaune na farko daya kare mata kallo, ya ciro wayan shi yayi snapping dinta, ta gyara kwanciya veil din kanta ya zamo kasa, gashin kanta ya zubo ya rufe mata kakkyawan fuskan ta, da sauri yasa hannu ya matsar da gashin gefe, karaf ta tashi sukayi ido hudu dashi, ya tsakar mata lausassar murmushi, "ta lumshe ido tana kallonsa wani irin sanyi take ji azuciyar ta, dakyar ta mike, ta Harare shi "tace miye haka zaka tabani? ? Dariya ma ta bashi, ya mika mata papers din yace kiyi abunda kika ga dama dasu, ta bata rai ta amsa ta ciro pen a jakarta tayi signing ta mika mai, ta tashi tace sai anjima, yace "babu ko godiya, tayi banzan dashi ta wuce zata fice, takasa bude kofa, ta danna lock din yaki budewa, ta juyo ta kalle shi a fusace tace "nakasa bude kofan, yayi dariya ya taso yace d door is open kece dai yar kauye baki iya budewa ba, yasa hannu xai bude kenan aka bango kofan daga waje kursum ta fada jikin shi a tsorace😳😳😳
Zee dana gama kulewa ganin kursum jikin masoyinta yasan ta kara fusata😡😡,tace yaya yazid dama shegian yarinyan nan ce a office dinka tun dazu, shine secretary dinka ta zauna dani office dinta tun dazu akan cewa kana da important visitor, gajiya nayi da jira shiyasa nayi deciding in shigo kawai, ta fashe da kuka😭😭😭😭
Ya yazid kasa magana ma yayi dan haushi, dan dama haka take shigo mai office duk lokacin data ga dama,"kursum ta karaso wajenta da sauri tace "kiyi hakuri, wlh ba abunda kike tunani bane, aiki ne yakawo ni nan ba komai ba" zee ta Harare ta tace karya kike munafuka dama daga ganinki ke yar bariki ce, mayya yar titiiiii.......bata ida magana ba ya yazid ya wanketa da mari saida taga wuta🔥, tace baby ni ka mara? Yace namareki din, ba sister dinki bace atleast respect her for once, "kursum dai tana gefe bata ce masu komai, zee tana kuka tace baby dan ina sonka dayawa shiyasa kakemin wulakanci, ta kalli kursum tace ke kuma hajiya na asibiti ba lafiya kinzo nan kina cin amana, toh baki isa ba kuma sai na koya miki hankali ta fice , da sauri itama kursum ta bita tana kwalla mata kira.
Yana nan tsaya yaji wayar shi na ringing ya duba yaga umma,da sauri ya dauka suka gaisa, tace my son I hav been trying ur line bai xuwa, kana ina ne? "Yace ina office umma, tace to kazo ka sameni a asibitin dr malik yanxun nan, hajiya hadiza ce ba lafiya, yace toh ganinan umma, ya ajiye wayan da sauri yadau mukullin mota ya fice.
Har bakin mota ta biyota tana zee kiyi hakuri mana, ki taimaka ki kaini asibitin banzo da mota ba, zee tayi banza da ita ta shige mota abunta taja a fusace😡😡
Haka ta karaso bakin titi kozata samu taxi, shiru dai bata samu ba ga wani irin ciwon kai dake damunta, tana tsaye wata hadaddiyar jeep kirar classic 2020 taxo gabanta, yayi wining glass din motan, yace little witch shigo in kaiki, tayi banza dashi, yayita mata horn taki kulashi, da daga dai zai kara mata ciwon kai tayuwo tace ya yazid miye haka, nace bazan shigo ba ka wuce kawai, "yace asibiti zani wajen hajiya kema nasan can zaki je, kizo in maki lift dan bazaki samu taxi anan ba, ta tsaya tunani, ita dai bataso zee ta kara ganin su tare, haka dai ta hakura ta shigan motan.
Har suka iso asibitin babu wanda ya yiwa wani magana, ta fito da sauri zata wuce ciki, yace ke kinsan inda aka kwantar da ita ne? Tace a'a, "yace to saiki jirani ai tunda ni nasan wajen, duk sai taji kunya, haka suka jero har inda umma ke zaune, ya karaso gabanta yace umma lafiya dai ko? Tace eh hajiyan ta farfado, yanxu bacci take ma, shehu yana wajen doctor jin meke damunta, kursum dake bayanshi ta karaso ta gaida umma da mata godiya sosai akan kokarin datayi na kawo mamanta asibiti, umma dai sai kallonta take dan batasanta ba, tace my son ina kasamo pretty girl dinnan, yazid yayi dariya yace ai sumayya ce diyar hajiya, na rage mata hanya ne,"umma tace ikon Allah dama ni ban taba ganinta ba, ya kike sumayya? Kursum akunya ce ta amsa tace lafiya kalau, umma dai sai murmushi take, ji take kaman tasan ta, wani irin son yarinyan taji har cikin zuciyan ta.😀😀
Baba shehu ne ya fito yasame su yake gayamasu ai jinin hajiya ne yahau sosai dalilin firgeta da tayi, dan yanxu haka ta farfado amma har yanxu tana tare da shock,"ya kalli umma yace haijya mairo bata gayamaki abunda ke damunta ba kafin ta suma, umma tayi shiru batace komai, baba shehu yace toh Allah ya bata lafiya shine kawai fatan mu, yanxu dai doctor yace mutum daya zai zauna da ita, inya so gobe mazo mu ganinta, ya kalli kursum yace ke kizauna da ita harta tashi, hajiya mairo kuna iya tafiya tunda sai gobe za'a iya ganinta, "umma tace to shikenan bari mu wuce, gobe saimu dawo, my son let go, ta kalli kursum tace sumayya ki kula da mamanki sosai kinji, tace toh umma zan kula da ita sosai.
baba shehu yace zan turo samira ta kawo muku abunda zaku bukata,tace toh"ya wuce abun shi.
Har sun wuce ya yazid ya dawo da sauri yace Karki zauna kina game, akula da marar lafiya dai, ta murguda mai baki tace ina ruwanka toh😕😕...... yayi dariya yace zanyi maganin tsiwan nan naki, ya fice da sauri......
Ta tura kofan dakin ahankali, ta karaso gaban gadon da take kwance ga ruwan drip an daura mata, ta zauna kusa da ita ta riko hannun ta , tana mamakin abunda ya firgita hajiya da jininta ya hau sosai, duk sai taji tausayin hajiya ya kamata, batasan lokaci da ta fara zubda hawaye ba😭, burinta kawai Allah ya sada ta da maihaifiyar ta wataran koda amafarki ne.
Digan hawayen da hajiya taji ahannu ta yasa tafara motsi tana kokarin bude ido, ahankali harta bude idonta, ta kalli kursum dake kuka, afirgice ta tashi ta ruko hannun kursum tace "Kursum ashe baki mutu ba"
Agigice kursum ta dago ta kalle ta...........😳😳😳😳
Rudani, tashin hankali, faduwar gaba, lokaci guda ta shiga😳
🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺
🌺🌺 By ~ Xarah Bêê
page 5⃣4⃣✨
Hankali tashe Tace "hajiya nice sumayya ba kursum ba, amma sam hajiya batasan inda kanta yake ba, ihu sunan kursum kawai take, doctor ne ya shigo dakin da sauri jin ihu ta, ya tsira mata allurar bacci. Ya kalli kursum yace"wace mai sunan da hajiya ke kira? "Tace nima dai doctor bansani ba,ko adangi banji mai sunan ba, "ya nisa yace tabbas mai sunan tana da alaka da shock din da hajiya tashiga, amma karki damu idan ta tashi she will be normal, "tace toh dr mungode, ya fice. Itama taja kujera ta zauna tayi tagumi, tunanin ta daya wace kursum din da hajiya ke ambata, dan tunda take da sumy bata taba mata xance wata kursum ba.
Ranta abace ta iso gidan aminiyar ta tana kuka, meerah dake baje afalo daga ita sai bom short da bra ga uban giya agabanta, " ta ajiye cigarette din hannunta, ta karasao wanjenta dasauri,"tace zee mi aka miki? Miya faru? Kukan mi kike?
Zee takara fashewa da kuka tace "girlfriend wai yau ni ya yazid ya mara akan wata shegia yarinya, "meerah ta kwalala ido waje, tace babe gayamin wace yar iska ce yanxu in maki maganinta, "zee ta gyara zama ta zayyane mata komai akan sumy, "meerah tayi kwafa tace lailai galfrnd, akan small brat dinnan duk kika birkeci, yanxu abunda zamuyi shine gobe muje har school din da aka jefar da ita a bauchi mu binciki past dinta, dan na tabbata she will have some dirty secret da take boyewa," zee tace nima dai I dnt trust her, dole mu samo abunda zamuyi using against her, "meerah ta zuba giya a cup ta mika mata,tace just drink diz banason ganinki haka plz, chill up babe akwai casu anjima, " ta amsa tayi murmushi, ita dai tana son meerah sosai cox she is always there 4 her.
*wace ce meerah*
Asali sunanta Amirat oyekola, haifaffiyar garin lagos ce, sun hadu da zee a lagos state university inda department dinsu guda, ganin zee yar masu kudi ce marar wayo yasa ta shishige mata har suka zama best friends, duk wata harka ta shaye shaye da clubbing saida ta koya mata, taso tasa zee a harkar bin maza amma taki yadda. Sun kare degree ta tattara tabiyo zee kano har gidansu, acewarta ta gaji da talaucin iyayenta, "haka tayita harkar kawo samari gidan, daga karshe hajiya ta koreta tabar gidan, wani daga cikin samarinta suka kama mata gidan da take yanxu.
*cigaban labari*
suna zauna a parlour suna hira "yace umma barin leka huzaifa kwana biu bamu huda ba, tayi murmushi tace a daren nan, gayamin gaskia dai kodai gurin sumy zaka, dannan lura da kallon dakake mata dazu, ya sosa keya, "Allah umma wajen huzaifa zani kuma yarinyan nan babu komai tsakani na da ita,"tace to son saika dawo, "kaima dai yakamata kayi auren, ga abokinka ya dade da aure shiyasa ma ya rage zuwa nan,"yayi dariya yace umma karki damu very soon xanyi, ya fice.
Zaune suke suna cin abinci sukaji knocking din kofa,ta tashi da sauri ta zura hijab taje ta bude,"tace ya yazid yau kaine a gidanmu sannanu da zuwa, "yayi dariya yace amarya bakya laifi, ya karasa ciki, huzaifa yace "aina dauka yauma baza ka zoba aiki yama yawa, yazid yace toh gashi nazo kuma dama yunwa nake ji, nazo adaidai, "huzaif yace to ai xama zakayi mu baje, "salma dai dariya kawai take dan tasan basa wasa da abinci.
sun gama Ci suka hau hira, huzaifa ya yace "angon zee wai yaushe xamu kawo maka itane, yazid ya bata rai yace "zee ko matsala, banma gayama ba hajiyarsu ba lafiya tana asibiti, huzaifa yace kace suruka dai ba lafiya, "yazid ya kaimai duka yace nifa bance maka zan auri zee ba, "Salma tace gaskia ya yazid zamu biya gobe mu dubota duk da bana shiri da xee, "huzaifa yace kodan darajan amintakar su da umma yakamata muje, "yazid yace to Allah ya kaimu goben, xan biyo sai mu wuce, ya musu sallama dare yayi ya wuce.
samira ta kawo masu komai da zasu bukata, wajen 10pm doctor mallik ya shigo dubata, "ta tashi jikin da sauki, ya kalli kursum yace,"data farka ba tace komai ba? "tace eh, ya mika mata magunguna, yace wanna joltan valsartan 160 mg na hawan jini ne, zata na sha sau daya a rana, Aspirin cardio 100mg zai taimaka wajen narkar da jini daya hau kanta shima sau daya zata sha, ku tabbata tasha su, "tace toh Dr nida kaina zanna bata, "yace jikin nata yayi sauki gobe xan sallame ku, "tace Allah kaimu ya fice.
tashi tayi ta ninke kayan sallarta ta ejiye gefe, ta karaso gaban hajiya dake Zaune tayi tagumi, "tace hajiya sannu kina bukatan wani abu?? tace taimaka min in watsa ruwa kawai. "ta rike hajiya har toilet ta watsa ruwa tayi alwala ta fito tafara sallolin..
*washe gari*
Duk sun hallara a asibiti umma na zaune kusa da hajiya suna xantawa kasa kasa, kursum na gefe tana hada musu kayansu waje daya, shi kuwa oga yazid ya kame kan kujera yana waya ya zuba mata idanu,"da sauri ya tashi yace umma barin je in shigo dasu huzaifa suna waje" tace to my son," ta kalli hajiya tace bakwa hira da sumy ne ?? naga tunda mukazo tana gefe tayi shuru, hajiya taya tsine fuska tace "ina ruwana da ita" umma tace haba hadiza tunda kin rasa yarki Ai ya kamata kija sumy ajiki tamkar ke kika haifeta, tsaki hajiya tayi tace nifa banason ta, xan jata ajiki kawai dan inji labari kursum daga bakinta.
yazid ya shigo tare da huzaifa da salma, suka gaishe da umma da hajiya, umma tace angama amarcin kenan tana zolayan salma amarya, huzaifa yana dariya yace kakus (sunan dayake Kiran hajiya) an tabo file kenan, ya jiki ? hajiya ta harare shi ta tace" nagaya ma ban tsufa ba har yanxu am 16 kana cemin kakus, gaba dayan su saida suka dara, sai sannan suka lura da kursum dake dariya daga gefe, huzaifa ya kalleta yace yammata daga ina ? tayi banza dashi, "yace umma ina kuka samo yarinya mai kama da kakus, yazid yayi caraf yace ai yarta ce, zai sake magana hajiya ta wullo mai harara, ba shiri yayi shuru, "salma tace nikam nasamu kawa, takarasa wajen kursum, tace kawata bakya magana ne? kursum tayi murmushi tace "inayi mana yakike ? ni sunana sumayya, "salma tace gaskia naji dadi saninki dama banda kowa agarin nan, kursum tace u are welcm nima am happy to meet u. .........huzaifa na gefe yana waya, yazid ya karaso wajen su ya zauna, ya kashewa kursum ido yace "my witch anyi sabuwar kawa an manta dani koh ?? ta bata rai ta murguda baki tace ina ruwana dakai, u are my enemy not a friend, yayi dariya yace bakisan enemies na zama best frnds ba, "salma dai bunsu tayi da Ido, "huzaifa ya gama yace"umma nizan wuce ana naima na a office, tace to son kayi kokari ma, ya kalli hajiya yace kakus get well soon, "salma ki zauna tare da kawarki later zanzo in dauke ki, tace toh , yabi kursum da kallo ya fice, yazid daya lura da abokin shi, yatashi fuska a daure yace umma sallaman sai yaushe ne? nafara gajiya da zaman asibiti, "hajiya tayi caraf tace kaga yaro da rigima, ai tunda bagaka zee ba dole ka damemu, idan ka gaji kaje waje ka zauna mana, "a fusace ya fice yayi waje dan yasan halin hajiya, "umma tace kwantar da hankalin ki, keda baki da lafiya miye na tada jijiyar wuya, " kursum dake jinsu bata ji dadin abunda hajiya tace ba, kaman ta fita ta bishi amma ba dama...
Baba shehu ne ya shigo da takardar sallaman hajiya, yace su zo su wuce ya sauke su gida, kursum da salma suka kwashi kaya, umma ta taimakawa hajiya ta mike suka fice, "yana zaune cikin mota, umma tashigo tace muje koh, yace su hajiya fa ? tace suna motan shehu, muje gidan "yace toh umma.
sun iso gidan, samira ta fito da sauri ta gaishe su ta kwashi kaya tayi ciki dasu, kursum da salma suka shigar da hajiya, baba shehu ya juya ya koma office. "umma tace son bazaka shiga gidan bane, "yace umma barin jiraki anan kawai banason shiga ga mitar hajiya ga kuma zee da rigima nasan tana ciki, "tayi dariya tace yau kuma zee ake boyewa, to barin shiga agurguje in fito, ta wuce shi kuma ya karasa garden ya zauna. .......
Sauri suke ta karaso gida ta canxa kaya su wuce bauchi , tun sassafe su kayi niyya tafiya, till dawn party din da sukayi yasa su bacci har rana, meerah tace galfrnd kiyi parking a waje kawai ki shiga ki canxa kaya ki fito mu wuce kar muyi dare, " zee tace karki damu babe bazan jima ma," meerah tace yauwa karki manta da kudaden dazaki kwaso, tace toh
hajiya da umma na sama adaki suna xantawa, kursum da salma suna parlour suna hira, "samira ta sauko tace antee sumy umma na Kiran ki, kursum ta tashi da sauri ta haura sama, ta shiga dakin da sallamanta, umma ta amsa da fara'arta tace yauwa sumy yayanku na waje ki kaimai ruwa yasha,"tace toh ta fice, taje kitchen ta dauko bottle water ta fita haraban gidan, can ta hango shi shinkide kan kujera, ta karaso, "idon shi rufe da alama bacci yake, tayi murmushin mugunta ta bude roban ruwa zata tsiyaya mai a fuska, "karaf taji ya rike mata hannu gam saida ta tsorata, ya mike tsaye yana kallonta,"tayi karfin halin cewa miye haka na rikemin hannu, yace ai yau bazan sake kiba saikin gayamin dalilin dayasa kike cemin am ur enemy, "tayi shuru batace komai ba.
Agurguje tayi parking awaje, ta shigo gidan da saurin ta, gabanta saida ya fadi hangosu tare rike da hannu ta, wani irin bakin ciki ya mamaye zuciyan ta, wato yarinyan nan bazata fita harkar saurayina ba, lailai kuwa I have to destroy her once n 4 all, ta karasa parlour da sauri dan karsu ganta, bata ankara ba taji salma tace "zee daga ina haka ? saurin mi kike ?? "ta juyo a fusace tace I don't owe u any explanation, dan kina matar abokin yazid dat doesn't give u d right to interfere in my life, taja uban tsaki ta wuce, salma kam bataji haushi ba, tasa ba da cin mutuncin ta, dan farkon haduwan suma ce mata tayi she is 2 local tayi harka da ita. hmm
ko dakin hajiya bata shiga ba ta wuce dakin baba shehu ta kwashi kudade masu yawa da papers na address din makarantar sumy, ta wuce dakinta tasa wasu matsatsun english wears marasa mutunci, ta sauko koh kallon salma batai ba ta fice, "salma tace Allah ya shirya, gaskia dai ya yazid baiyi saan mace ba.
koda ta fito suna nan tare, saidai yanxu zaune suke da alama hira suke, tayi kwafa ta wuce waje, taja mota sai bauchi, meerah na magana ko kollanta batai ba, sharara gudu kawai take.
kinyi shuru baki ce komai ba, tace to ya yazid me kakeso ince, nidai kawai I don't like u datx all, yayi dariya yace karya kike nasan kina sona, ta bata rai ta tashi zata tafi, yace my witch karki tafi zauna in baki labarin rayuwata, "ta kara tamke fuska ta zauna tace ina jinka, "yace kinsan dai no one is perfect koh ? ta girgiza kai alaman eh ,"yace ni nan da kike ganina nayi making alot of mistakes arayuwana wanda har yau am still regretting, "akwai wata yarinya dukda na manta sunanta, but I will never forget her smiling face, ya gyara zama zai cigaba da magana umma ta fito tace mai su tafi , ya tashi ya killi kursum yace next time idan mun hadu zan karasa miki, "jikinta a sanyaye ta bishi da ido tace toh, ya wuce, tayi shiru tana tunanin, wato ya yazid bai manta da sumy ba, amma meyasa bai dawo gareta ba ko sau daya ba ??
jiki ba kwari ta shiga ciki, salma tace ke kuwa daga kai ruwa kin makale, kursum tace aiko ban dade ba, "muje dakina muyi hira zaman parlour ya isheni, suka wuce daki, salma ta dale gado tace "anya sumy ya yazid ba sonki yake ba, "kursum tace haba dai, aini ko sona yake bazan yadda ba, saboda he is really good at playing women's heart, "salma ta kwalalo ido tace dama kinsan shine ,"da sauri tace a'a, salma tace au nayi mamaki ne, dan ya huzaifa ya taba gayamin ya yaudari mata ba kadan ba amma yanxu kam ya daina, mata basa gabanshi."kursum ta sauke ajiyan zuciyan, aranta tace Allah yasa dagaske ya shiryu.
Sun iso bauchi around 6pm direct makarantar suka wuce, suna zuwa har office din gimbiya Hafsatu aka gaisu, gimbiya na zaune rai abace sai hada tarkacen ta take waje daya, suka shigo da fara'arsu suka ja kujera suka zauna, ta kalle su tace kuna bukatan wani abune yan mata ? zee tayi shiru, meerah tace mu yan garin nan ne, dama cigiyar kawarmu muke, munaso kidan bamu details akanta na zamanta a makarantar nan. gimbiya ta nisa tace miye sunanta ? zee tace sumayya tanimu bawa, "gimbiya ta kare masu kallo aranta tace karya suke, dan sumy bata da wasu frnds sai kursum, kuma daga gani yan bariki ne, kila sunji labarin dukiyar da ubanta ya mutu ya bar mata shiyasa suke naiman ta suci arziki, toh Basu isa ba nice xanci arzikin nan.
Tace yammata sai dai kuyi hakuri record dinmu confidential ne bama fitar dashi, "zee zata fara roko meerah ta tabo ta tayi shuru, meerah ta bude jakar xee ta fiddo da makudan kudi ta tura su gaban gimbiya tace ko nawa kike so zamu kara miki ki gayamana abu akanta kawai, "gimbiya tace lailai yau na hadu dayan duniya, ta masu kallon banxa tace ku fice mun daga office kafin insa ayi waje daku, Meerah tace toh xamu tafi, ta dauki paper ta rubuta mata contact dinsu incase in ta canxa mind din gayamasu wani abu, suka fice. gimbiya taja tsaki ta dauki paper tasa a dust bin, ta kwashe kudin tasa a jakar ta, "dama naiman kudi take ido rufe, saboda gwamnati tayi seizing licences dinta na makarantar akan zarginta da ake na saida dalibai," tayi murmushi tace sumy amfanin ki yazo rayuwata, ta binciko file din sumy ta kwashe address din gidan su.......ta kyalkyale da dariya tace gobe sai Kanon Dabo
😳😳😳😳Hmmm tashin Hankali
kursum get ready gimbiya na hanya.
*Xarah Bêê*😘
*Dedicated to bady social*
~Luv u all~😘😘😘
[05/09 12:52 pm] xarah bukar✍🏻✍🏻:
🌺🌺🌺KURSUM🌺🌺🌺
🌺🌺By ~Xarah Bêê
Page 5⃣5⃣
Da daddare huzaifa yazo daukan salma, har bakin mota kursum ta rokata,suna ta hira da dariya kaman dama sunsan juna"ta gaida shi ya amsa da fara'a sa yana tsokanar ta da autar kakus (hajiya),tayi dariya tamasu sallama ta koma ciki........
Bayan kwana biyu jikin hajiya yayi sauki, "kursum ta shigo dakin rike da magani da ruwa, tace hajiya lokacin shan magani yayi "ta ya mutse fuska tace maganin sai dacin tsiya a dole kawai nake sha, tayi murmushi ta zauna tabata maganin da ruwa tasha sannan ta gyara mata kwanciya, zata fita hajiya tace Sumy kawarki da kukayi accident, ta rasu iyayanta sun sani kuwa? Dam gaban kursum ya fadi, ta dawo ta zaune tace Ai marainiya ce bata da kowa, dama gidannan zamu zo, "jikin hajiya yayi sanyi,da gangan dama ta tambaye ta Dan taji labarin yar'ta ,ta nisa tace Allah yaji kanta amma ya akai tayi surviving a skull din tunda kince bata da kowa "kursum dake sharar kwalla tace abun tausayi ko kayan sawa gimbiya bata siyamata saidai Sumy ta bata akayanta,excursion ma baa zuwa da ita,tunda bata da kudin biya," hajiya tace wace Sumy CE ke bata kaya? Kursum data gano kuskuren magananta tace ni mana Nike bata kayan. Ran hajiya ya gama baci, aranta tace wato diamonds din da akaba gimbiya cinyesu tayi,alhalin ko wana diamond worth 2.5 million ne ,shine ko kayan sawa bata iya siyawa yar'ta, wani irin tsanar gimbiya taji......"ta kalli kursum tace ke tashi ki ficemin daga daki ,"kursum tace daga hira kuma sai kora kaman nayi laifi ,ta tashi sum sum ta fice, tana mamakin halin hajiya wataran ayi hirar arziki wata ran kuwa ba mutunci...
Kina ganin akwai Hope kuwa,kwana biyu da dawowan mu amma shuru matan nan bata Kira ba, "meerah tace haba zee duk kin tada hankalin ki, idan ma bata kira ba zamu samo wani mafita, zee tace ai dole in damu dan yanda nake ganin taketaken ya yazid zai iya rabuwa dani ya komawa Sumy, meerah taja tsaki tace karfa ki manta tun farko dama baice yana sonki ba,kece kika makale mai, so don't be surprise idan ya rabu dake, zee ta bata rai tace koda na makale mai aiya kulani, kuma yanxu Gidan su zani coz nasan he is still angry with me ko calls dina bai picking ,ko kallon meerah batai ba ta suri Jakarta ta fice.........
Zaune suke a dinning suna lunch, Umma tace "son hurry up ka wuce airport saura 1hour flight din abbanka yayi landing, banaso ya jiraka, "yace toh umma ina gamawa xan wuce," bugun kofa sukaji anayi da karfi, umma ta kwallawa hajara (mai aiki) kira taje ta bude,"tana budewa zee ta ban gajeta ta shigo ciki tana kwalla wa ya yazid kira batama lura dasu ba, umma ta bata rai, azuciyan ta tace dama nasan sai crazy girl dinnan, dan haushi fasa cin abinci tayi ta tashi zata wuce, "yazid yace umma baki ci komai ba ? Tayi banxa dashi, sai sannan zee ta lura dasu,ta karaso da sauri tace baby ashe kana nan shine kayi shuru,ta kalli umma tace sannu," umma ta balla mata harara ta wuce.
Taja kujera ta zauna ta tace "baby miyasa mom dinka ke treating dina lyk nobody kaman ba future in-law taba, "ya tamke fuska yace" Ai baki taba gaishe taba iyaka cinki sannu, sannu ko ba gaisuwa bace, ta turo baki tace "nifa ko babana bana gaisarwa balle ita, bata isa ba, yazid daya gama fusata ya mike tsaya yace uwartawa CE bata isa ba ? hankali kwance tace Yes, " Rai abace yace ban taba sani u are crazy ba saiyau ya dauki car keys zai fice, tayi saurin riko hannun shi ta rungumo shi ta baya tace yes am crazing in love with you, "a fusace ya tureta,ya kalle ta yace diz is not love,u are only obsessed with me, infact nida ke it over......what ta fada a firgice tace are u breaking up wit me? Yace yes,ko juyowa baiba ya fice abunshi. Duniyar gaba daya tai mata zafi, kuka take rusawa ta shiga fasa plate da cups dake kan dinning ,tabbas tasan saboda Sumy ya rabu da ita,amma tayi alkawarin bazai taba samun taba cox sai tayi destroying life dinta, sai zage zage take kaman tababbiya.
Umma dake daki ta fito da sauri jin fashe fashen yayi yawa, ganin zee na displaying madness yasa ta kira hajara tayi waje da ita.....zee tace basai anyi waje dani ba, nasan hanya, kuma nasan makircin kine yasa ya yazid ya rabu dani, "Allah ya shiryeki kawai umma ta iya ce mata, taja tsaki tabar gidan.
Office din baba Shehu ta wuce, yana zaune yana waya ta banko kofa ta shigo tana kuka, ba shiri ya ajiye wayan ya karaso gabanta yace zainab kukan mi kike ? Ina kika shiga kwana biyu ban ganki ba ?" Cikin kuka ta tsara mai komai har zuwan su bauchi, baba Shehu yayi dariya yace halina dake u ar alwyz crazing bakya Abu da tunani, "ta bata rai tace Baba ka daina cemin am crazing ina da hankali, I don't knw y mutane ke cemin banda hankali, yayi shuru yana tunani, koda ya auri jamila (maman zee) tana da mental illness harta rasu, shiyasa sumtymz zee take abu kaman mai hauka, ya nisa yace ," am sorry auta ta....ta kyalkyale da dariya tace to baba yanxu miye mafita, yace karki damu zan tura private detective dazai binciko miki komai akan ta, tun daga ranar da aka kaita school din, abunda kikeso kenan koh ?da fara'arta tace eh, yace toh yanxu abu biu zakiyi idan kinaso komai ya tafi daidai, da sauri tace me ? Yace dole ki nunawa yazid kin hakura dashi sannan kuma kija Sumy ajiki yadda bazata gane abunda kike shirin yiba, ta kwalalo ido waje tace"gaskia baba bazan iya, yace toh ke kikasani tashi ki tafi,"ta ma rairace fuska tace na yadda xanyi, yace toh ki wuce gidan kafin in zo tace OK ta fice da murnan ta...... Shima sai murmushi yake dan perfect tym yake jira ya kawar da Sumy once n 4 all.
Washe gari, hajiya na zaune a parlour tana cin abinci, zee na kallon TV, kursum ta sauko zata wuce office kusan kwana biu bata jeba, ta gaishe da hajiya ,"ta amsa a yatsine ne ,zee dake gefe tace my sis har zaki tafi,kursum da taji maganan bambarakwai,tace eh ta masu sallama ta fice.
Zata shiga mota taji hayaniya abakin gate, ta karasa wajan da sauri, mai gadi daya hango tana zuwa, ya kalli matar dake tsaye da Da niki nikin akwatuna, yace yauwa ga madam Sumy nan zuwa kwayi magana dan bazan bari ki shiga gidan nan ba,"gimbiya tayi shewa tace gidan nan shiga daram.
Tana leka waje sukayi ido hudu da gimbiya hafsatu,dam gabanta ya fadi ,gimbiya data gama tsorata tace baki mutu ba dama........
Da sauri kursum taja ta gefe ta tace mi ya kawo ki gidan nan, gimbiya tace aike xan tambaya kin mutu miya kawoki nan,INA Sumy ? Kursum tace ai Sumy CE ta rasu bani ba, yanxu haka yan gidan sun dauka nice Sumy, long story ne idan mun zauna xan baki labari ,"ta bude Jakarta ta zaro makudan kudi ta mikawa gimbiya tace ga wannan ki koma bauchi yanxu nan, zamuyi waya......gimbiya ta kece da dariya tace Ai baki isa ba, babu inda zani, kursum tace koki tafi ko in kira securities su fitar dake daga nan, "ta kara kecewa da dariya tace ai ke zabi ya ragewa, ko ki barni in zauna a gidan ko kuma inje in tona miki asiri,kinga dagani harke mun rasa , balle ke da baki da wajan zuwa.
Kursum data gama kulewa tace Baza ki zauna a gidan ba, kiyi abunda zakiyi. Gimbiya tace toh zakiga Abunda zanyi kuwa, ta bangaje maigadi ta shige gidan da gudunta, Agigice kursum ta bita tana cewa tsaya!! Tsaya!! Muyi magana, amma ina.....gimbiya tayi nisa batajin kira, harta karaso bankin parlour ta tura kofa ta shiga........
Tashin sense 😳😳
*Xarah Bukar*😘
*Dedicated to Bady social*
~Luv u all~😘😘
No comments:
Post a Comment