Sunday, 30 October 2016

Kursum 56 to 60

[06/09 10:53 AM] Xarah Bukar ✍🏻✍🏻: 🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺

      🌺🌺 by ~ Xarah Bee

Page 5⃣6⃣✨

Hankali kwance ta tura kofan ta shiga da sallaman ta, hajiya ta amsa tace waye ? Zee ta juya taga gimbiya, tace baiwar Allah aida baki zoba kin kiramu ta waya, sai sannan gimbiya ta gane zee, itace marar kunyan nan da sukazo naiman labarin sumy, taja tsaki tace bansanki ba kuma ba wajan ki nazo ba, hajiya tace zee kinsanta tane ? Zee tayi shuru, hajiya tace bakuwa gurunwa kikazo ? Caraf kursum ta shigo tace gurina tazo, kuma a gidan nan zata zauna, hajiya tace bazata zauna ba, Ai nan ba hotel bane daza ki kawota, gimbiya tace haba hajiya nice fa gimbiya makarantar da Sumy tayi harta girma, yadda na kulan miki da ita bai kamata ki Kore niba, "ran hajiya ya gama bacci, wani irin  tsanar gimbiya taji a zuciyar ta,aranta tace wato matar nan itace ta maida min kursum abun tausayi ko kaya  bata siya mata. Ta nisa tace koda kike riketa aiba kyauta bane kudi aka baki, na baki minti biyar ki ficemin daga gida.....

Gimbiya ta kalli kursum tamata signal kotasa baki ko kuma ta tona, " kursum tayi Gyaran murya tace gaskia hajiya saidai kiyi hakuri, dole gimbiya ta zauna agidan nan, tunda gidana ne, "hajiya data gama fusata tace to na yadda ta zauna amma ba nan tare damu ba, ki kaita can bangaran masu aiki ta zauna, kursum zata kara magana hajiya ta daka  mata hannu tace nagama magana, ta dogara Sandar ta tahau ra sama.......kursum tace nizan wuce office ta fice,da sauri gimbiya tabi ta tace amma dai hajiyar nan bata da mutunci, kursum tace karki CE haka dan kuwa bata da matsala, kiyi hakuri ki zauna a part din masu aiki kafin insamo mafita, idan kika Kama kanki zakiji dadin zama da ita, makauniya ce ba gani take ba,gimbiya tace kina nufin duk  kwalliyan datayi da uban dauri da bakin glass din bata gani ? Tace kwarai kuwa,tun wajan shekaru 18 da suka wuce tasamu matsalan ido, gimbiya tace shikenan ki tura masu aikin su gyaramin dakin, kursum tace toh kayan ki ma xansa ashigo dasu, xan wuce aiki saina dawo.

Gimbiya ta koma parlour ta zauna, zee ta kalle ta taja tsaki tace ashe bakin ku Da ita shiyasa kika ki bamu details akanta, gimbaya tace yarinya ni kike  jawa tsaki ? Zee tace eh mana ke wace CE ? Gimbiya ta mike taje har gabanta ta kama mata kunne gam tace idan kina takama ke yar bariki toh ni sunana na biyu bariki, ki kiyaye ni danni ba tsarar wasanki bace,kina jina ? Zafin da taji yasa Ba shiri tace eh naji kisake mun kunne, saida taga kunnen yayi jajir sannan ta saki ta koma kan kujera ta baje, "da sauri zee ta tashi tace muguwa ta gudu sama...........

Agurguje plz........

Kursum ta koma bakin aiki, takan kiran inna taji ya hanifa, tsakanin ta da yazid sai wasa buya bata barin su hadu dan ta tabbatar ta kamu da son shi. tsoranta daya bai wuce kar asirinta ya tonu ba.

Hajiya ta warware sosai, bata shiga harkan kowa a gidan kullum tana makale adaki, kursum tana shigowa gaisheta ta bata magani.

Yazid ya kanzo gidan ganin kursum, amma sai dai yasha zama a parlour bata fitowa, idan yagaji ya tafi....

Zee kuwa basu da aiki ita da meerah sai clubbing da shaye shaye, takan  yi kwana biu bata kwana gida ba, ta fita harkan yazid ko sun hadu bata kulashi, dukda sonshi na nan daram azuciyar ta, har dakin kursum take shiga tayi ta janta da hira kaman gaske.

Baba Shehu na nan da kudirin sa, burinsa ya kawar da Sumy,amma ya rasa yazeyi.

Gimbiya hafsatu  ko yaushe tana main house abaje a parlour bata da aiki sai tsegumi, kowa haushin ta yake  ji  agidan, tunda taga Baba Shehu take shishige mai, ita adole tasamu mijin aure, shi ko kallon bata ishe shi ba.....

Bayan sati biyu

Umma ce  taxo gidan tayi knocking kofa, gimbiya dake kallon TV taja tsaki ta tashi taje  budewa, ta bude suka gaisa da umma, umma tace amma ke bakuwa ce koh? gimbiya ta Kare mata kallo tace wata sabon gani hajiya maryam ai bazan taba mantawa da fuskan kiba, umma ta kwalalo ido waje tace ina kika sannni nikam bansan kiba......gimbiya ta kece da dariya tace Ai dole kimanta ni, 18 years ago kika kawo min kursum tana jaririya kokin mata ne? Umma ta bata rai tace banganeki bane, me kikeyi a gidan nan ? Tace zama nazoyi mana Ai Sumy daliba tace, umma tace toh yanxu babu komai tsakani na dake, tunda kursum ta rasu, karki kara gani na kice kin sanni, gimbiya tace haba hajiya miya yayi zafi haka, ki bari muyi zumunci mana," tayi banza da ita ta wuce sama dakin hajiya.

Gimbiya tace lailai matan nan,aiko  saina juyo xancen da zakuyi, sadaf taje bakin kofan dakin ta kasa kunne...

Hajiya tace ashe  zaki zo, na dauka kokin mata dani, umma tayi dariya tace yanxu ma agurguje nazo Alhaji na gari Shiyasa kika jini shuru ,ya karfin jiki ? Hajia tace da sauki sosai, Ina son dinki kwana biu baizo ba.......umma tace indai yazid ne anjima kina iya ganin shi, ta duba agogo, nizan wuce office sai munyi waya,"tayi sallama da hajiya ta fice.

Gimbiya dake labe ta bar wajan da sauri, aranta tace oh kakkyawan yaron nan dake zuwa wajan kursum ashe danta ne, ta kwalalo ido waje, idan umma ce uwarsa kenan yazid da kursum are siblings basu sani ba, ta koma bakin kofan ta tura ahankali tashi ga dakin, hajiya na zaune kan gado tana kallan pictures din daddy tana sharar kwalla, bata ankara ba sai ganin gimbiya tayi gabanta, arazane tace miya shigo dake nan, gimbiya data cika da mamaki tace keda kike makauniya hw cms kike kallon picxx, hajiya duk ta kideme,da sauri tadau glass dinta ta maida, munafuka fice min daki kafin insa ayi waje dake, "tayi shewa tace ai  ina fita  xan tara kowa a parlour ingaya masu Karya kike 4 d past 18yrs, kina gani kuru kuru," afusace hajiya tace Fadi price din da kikeso in baki kiyi shuru da bakinki, gimbiya tace banason kudi idan kikamin abu biyu toh ur secret is safe wit me, tace mai kikeso ? Na farko inaso indawo main house da xama nagaji da zama part din masu aiki, na biyu kisa  Shehu ya aure ni, " hajiya taja tsaki, na yadda dana farkon, amma na biyu I don't tink zai yuyu, bazan ma kanina auran dole ba,balle ke yar bariki wace tayi aure wajan shida ta kasa zama, gimbiya data gama kulewa tace toh naji ,xan  baki time kisan yadda kikai ya aure ni, ta fice afusace kalaman hajiya sun bata haushi.

Agajiye ta dawo daga office tayi sallan magrib ta fada gado, ta dauki wayanta taga 10 missed calls da sauri ta tashi zaune ganin number inna sadiya, ta buga  ringing daya Inna ta dauka, jin kukan hanifa yasa kursum ta gigice, tace Inna miya sameta ? Kukan mi take? Inna tace wlh zazzabi ke damunta tun jiya munje asibiti amma ba sauki har yanxu shiyasa ma nake kiranki," hankali tashe kursum tace inna dare yayi balle inzo, Ki cigaba da lallashin ta, gobe da sassafe zanzo in dauke ta, Inna tace toh sai kinzo, sukayi sallama.

Tunani take yadda zata dawo da hanifa gidan, bata da wani mafita ,da sauri ta tashi ta sauka kasa, suna kan dinning suna cin abinci ,zee sai wani bata rai take ganin gimbiya zaune dasu tana wurga loma, ta kalli baba Shehu tace waimi matar nan keyi anan ? Hajiya tayi caraf tace ke bana son rashin kunya, kici abinci........kursum ta karaso ta zauna tace baba xan tafi bauchi gobe, ya kalleta lafiya dai ko ? Tace eh, inaso kasamo mun driver dazai kaini kasan ban kware sosai ba, "zee tace sister y not inkai ki, baba Shehu ya watsa mata harara, bazaki kaita ba, ya kalleta kursum yace karki damu zan shirya miki driver dazai kaiki gobe wajan 8am, tace toh nagode baba, hajiya ni xanyi tafiya gobe xanma doctor malik magana ya turo nurse dazata na baki maganin ki, " hajiya taja ta tsaki tace shekara zakiyi kenan ? tace a'a agoben xan dawo xanyi dare dai, tace to asauka kalau ta mike ta wuce Daki, Baba shehu ma ya tashi ya fishi, zee data gama kulewa tayi wurgi da glass cup din dake hannuta ta fice daga gidan.....gimbiya ta kalli kursum, amma zainab dinnan is crazy koh ? yauwa mi zaikai ki bauchi? kursum tace hmm hanifa xan dauko bata da lafiya," gimbiya tace tashin hankali idan kika dauko ta mi zaki cewa masu gidan, yarki zakice ko wa? Tayi banza da ita ta tashi ta wuce....

Wajan karfe dayan dare, tana parlour tana kallon TV, taji motsi kaman ana saukowa kasa, da sauri ta kashe wutan ta labe bayan kujera, taji yana waya "yace bala kajira ni bakin gate gani nan zuwa ya fice waje, gimbiya dake labe tace  shehu wazai gani a darannan, sadaf ta bishi ahankali har waje, baba shehu yace bala nasan zaka iya aikin shiyasa na samoka, gobe karfe 8am zakazo ka kaita bauchi, bala yace angama duk yadda kace haka zaai, "yace yauwa ashe ka gane, kasheta zakayi idan kunyi nisa ka jefar da gawar ta yadda babu Wanda zai gani, sannan kai kuma ka bace kabar gari, ya fiddo makudan kudi Ya damka mai, bala ya karba yace angama, sai nazo goben, sukayi sallama ya koma ciki da sauri.

Gimbiya dake labe tana jinsu saida ta girgiza, mamaki kawai take kowa da hidden agenda dinshi a gidan, hajiya mai karyan maganta, zee d crazy gal, ga umma da yar'ta amma bata saniba, shehu da nashi makircin, kursum dake using identity din dead Sumy, ta tabbata yazid yana da nashi unknw secret din, Wat a mysterious family.

Tayi kwafa ta koma ciki, tunani kawai take yadda zatayi saving kursum in 7hours, cox idan ta bari aka kasheta barin  gidan nan yakamata dole.

         *Xarah Bukar*😘

*Dedicated to Bady social*

~luv u all~😘😘😘

[08/09 12:20 am] Xarah bukar✍🏻: 😘

🌺🌺🌺 KURSUM🌺🌺

        🌺🌺 by ~ Xarah Bêê

Page 5⃣7⃣✨

Tun  7am ta shirya tama  hajiya sallama "ta fito haraban gidan jiran driver.
    "Gimbiya  sai kai komo take a daki tun bayan sallan asubah, ta leka waje ta hango kursum tsaye bakin mota tana jiran bala," can dabara ta fado mata, da sauri ta fice ta shiga dakin baba shehu ahankali, da alama yana toilet, sadaf ta karasa bakin gadon ta dau wayarshi ta ta binciko contact din bala driver," ta tura mai msg

``` "change of plans kazo by 10am"```

tana turawa tayi deleting ta kashe wayan ta ajiye ta fice da sauri, ta sauke ajiyan zuciya, atleast zata samu tym din samu mafita.

      "Yana fitowa ya shirya da sauri yadau wayoyin sa ya fice, " kursum dake tsaya ta karaso ta gaida shi, baba kasan 8am zan wuce, gashi  7.45 har yanxu baizo ba, "yace karki damu bala baya  wasa da aikin sa zaizo Yanxun nan, " toh baba Allah yasa karya bata min tym, sukayi sallama baba shehu ya wuce office, aranshi sai murna yake , yarinya zaman ki yazo karshe a duniya.

   "Sai leke take ta window ta rasa mafita, ta sauko  sum sum ta karasa wajan kursum dake tsaye rai abace, "tace anya bazaki hakura da tafiyan ba naga har 9 yayi driver bai  iso ba, " kursum ta kalleta tace haba gimbiya kinsan hanifa amana tace dole in dauko ta, gashi layin baba shehu off bansan yadda xanyi ba, "gimbiya tayi shuru tama rasa me zatace, fatan ta kawai kar bala yazo dan 30mins ya rage goma ta cika...

    "Hankali kwance yake driving har ya iso gidan, ya kudiri niyya yau saiya ganta koda zata makale adaki, kusan 3weeks kenan yana bibiyanta....

Suna tsaye yashigo, dukta daburce ganin shi, zata koma ciki da gudu gimbiya ta riketa tsam, Ai babu guduwa da zakiyi in har kinason ganin hanif dole ki rokeshi ya kaiki, kursum ta bata rai banason haka, bakisan banaso in hadu dashi ba, gimbiya tayi shewa, tace ahab  ai nasan kina sonshi kina kaiwa kasuwa, taja ta har wajan shi ta bude motan ta turata ciki, " yazid dake kokarin fitowa daga motan saida ya tsorata,Sam bai lura dasu ba sai ganin gimbiya yayi ta turo ta....

  "ya tamke fuska, miya haka ? zaki ji mata ciwo ne ? Ta washe baki tace ai nasan wajan ta kazo, sai ka kaita Inda zata, ta kalli kursum da tayi kicin kicin fuska a murtuke, sai ki gayamai inda zaki ta rufe motan ta koma ciki......

      "Yaja mota suka kama hanya, ya kalle ta yayi murmushi, my witch ina zan kaiki ?
     Kaman tayi banza dashi, sai kuma tace " bauchi zaka kaini...
  "Ya kalleta, hop all is well.
" tayi banza dashi
   Ya cigaba da sharara gudu, can yace miya sa kike guduna ?
    "Banason ganin ka ne
Ya murmusa yace Y
   " tace I hate yhu
Kinsan I hate lies, nasan u Luv me" I dunno y kike  cewa u hate me, gashi ni am deeply inluv wit u kina bani tough time.....
     "Tace hmmm I don't biliv, infact I don't trust yhu.
   Am serious, u can trust me yace mata.
Tayi murmushi, last tym da muka hadu baka karasa min labarin yarinyar nan da kuka hadu a bauchi ba, kace ka manta sunanta, kasan inda take yanxu ???
   " ya sauke ajiyan zuciya, matata CE just 4 a nyt, na aureta da kwana daya nasake ta, wat tace "kana nufin u wia once married n divorced ??
   " eh, dat was d biggest mistake da nayi arayuwata, koda na saketa na tafi nakara komawa in dawo da ita, amma it waz 2 late aka cemin ta sake aure tabar nigeria..
   Kursum dake sharar kwalla a boye, aranta tana mamaki waya cemai Sumy ta sake aure, ta nisa tace eyya iyayen ta suka gayama ta sake aure kenan ?
   "Yace a'a, bata da kowa agarin ma, wani jamilu dana tura naiman aurenta a makarantar su shina turo ya bincikomin ita, koda yaje director din tace mai ai tayi aure bata kasar....
" ya kalli kursum dake zubda hawaye, ya ciro hankie dinshi ya mika ta, kukan mi kike, "ta karba tace it a pity, umma tasan da faruwar haka ? Yace e tasani na gayama ta komai, tare ma muka so zuwa naiman yarinyar, amma she was so busy, " I hop duk inda take yanxu zata yafemun.
  "tace am sure ta yafemaka.
Kinsan tane, hw are u sure she has 4given me ?
      " nayi guessing ne kawai tace mai....aranta mamakin hali gimbiya take, wato ita tayi karyan cewa sumy tayi aure tabar kasar, wat a cruel woman, aiko tana komawa zata fadi gaskia, inyaso daga ita har gimbayan sabar gidan.
   "Ta dau wayanta ta kira inna, suka gaisa, ya jikin hanifa
  " Inna tace da sauki sosai yanxu bacci ma take,
   inna nima Ina hanya,
tace toh kursum Allah ya kawoki lapia, sai kinzo, sukayi sallama.

"Ya kalleta yace wace ce  Hanifa ????
     Ta fuske tace ya'ta CE,
Wat yaja birki da karfi, kina da aure dama ? tace banda shi asali ma ban taba yiba, amma inada Ya' yar shekara daya, dauko ta xanyi bata da lapia,
     " yayi shuru bai ce komai ba, yasan dai she is decent ,hw cms take da Ya' ba aure,
     Afusace ya tada mota ya dunga sharara gudu kaman xai tashi sama, ni phatee mai dauko rahoto saida na tsorata, wanga sheka gudu kaman ba gobe😳😳

Tana baje a parlour (as usual) tana taunar cingam kaman wata yar gidan mangwaro, zee dake kan dinning tana cin abinci ta ja tsaki tace tsohuwar banza haka zaki kare munafuka, "gimbiya ta nuna ta da yatse, ni kike zagi ? Zee tace kwarai kuwa mayya, ta tashi afusace ta kama zee tana duka, ihu take bazan kara ba ki kyaleni, ba mafita ta dankara mata cizo ba shiri gimbiya ta sake ta, da gudu tabar wajen.
   " gimbiya tayi kwafa, shegian yarinya nakusa zama uwarki, ubanki ya shigo hannu na dole ya aureni ko yanaso ko baya so😍

              *Xarah Bukar*😘
   *Dedicated to Bady social*

~luv u all~😘😘😘

🌺🌺🌺 KURSUM🌺🌺
     
       🌺🌺 by ~ Xarah bêê

page 5⃣8⃣✨

Babu wanda yace uffan har suka iso garin bauchi, direct gidan inna sadiya suka zarce, "yayi parking yace karki dade cox bana nyt driving,
     " baza ka shigo ku gaisa da inna ba?
      no need, jux hurry up ki fito mu wuce, xan shiga masallaci
    Toh kawai tace ta shige gidan.
Inna na tsakar gida tana wanki taji sallaman ta, ta amsa tace amma dai kinyi saurin isowa
    "Kursum tace eh wlh inna ya kuke?
   lapia lau, taja ta suka shiga daki, hanifa na kwance tana Bacci, yanxu kam  xaxxabin ya sauka sosai, saidai bata son cin abinci inji inna
      " kursum ta nisa tace ai rashin cin abincin nata nada muna, ina isa gida zan kaita asibiti,
     "inna tace barin kawo maki naci da sha
   Kidai barshi wlh, muda muke sauri sallah kadai xanyi in wuce, inna tace irin sauri haka, bara na zubo maki ruwa a buta.
     "Bayan tayi sallah, sukayi sallama da inna tare da bata makudan kudi ta kula da kanta, tadau hanifa suka fice, inna sai zuba godiya ake.

"tsaye yake bakin mota yana waya da umma
  " son kace tana da ya' marar  lapia ?
    Haka dai tace min.
Okay don't bother asking her anytn, irinsu nasan situation dinsu, kuna isowa kano ka kaita asibiti, xanzo insa meku
     "Yace toh.
Hey ka gama wayan can we go ya juyo yaganta zaune cikin mota, wen kika fito ko motsin kin ban jiba
    " nayi kusan 10mins anan ai, "yayi murmushi ya shiga mota, ya kalli hanifa dake bacci jinkinta yace ur baby is cute😘
       tnx kawai tace,
suka Kama hanya🚗

Baba shehu zaune a office, ya kalli agogo yasan by diz tym she is already dead, wayashi ya dauka zai kira bala driver, yay mamaki matuka gannin wayan nashi kashe, yasan dai baya kashe waya, da sauri ya kunne ya kira bala, bugu daya ya dauka
    " ina fatan dai ka cika aiki?
     Bala yace wana aiki kuma, naje gidan around 10 wata Mata tacemin ai kace anfasa tafiyan sai gobe, nayi kokarin kiran ka layin kashe
   "ya tamke fuska, kaida nacema 8am maiya kawo ka 10, kuma wace tacema anfasa tafiyan?
      bala yace ka turomin msg inxo by 10am, ni bansan matar ba, amma daganin ta yar gari ce.
   Afusace ya tsinke call din ya dauki car keys dinshi yayi waje, yasan babu tantama gimbiya ce ta ruguza mai plans dinshi, amma hw cms tasan komai, lailai ko sai ya koya mata hankali.

Tana zaune kan dinning ta hada varieties of abinci sai wurga loma take, ya banko kofa ya shigo, saida  ta tsorata ta mike tsaya, shehu lapia ?
   Ko sauraron ta bai yiba, ya cafko wuyan ta ya shake, bana hanaki shiga tsabga taba
    " gimbiya dake kakarin shedewa tace kashe ni zakayi kenan kaman yadda ka tura akasheta, " ba shiri ya tsake ta ya wurga mata harara, bangane me kike nufi ba
       tayi shewa, shehu karka raina min yawo, ta fito da wayatan ta kunna mai zancen su da tayi recording, "yayi tsuru tsuru,
           toh mai zakiyi dashi?
     "ta kece da dariya, police station zan kai yanxu kuwa, " haba hafsatu mi yayi zafi haka kiyi hakuri mana....ta balla mai harara, aurena ko prison sai ka zabi daya
      "Ya kwalalo ido waje, are u trying to blackmail me.               za tayi magana hajiya ta sauko, lafiya nake jin hayaniya? gimbiya tayi caraf tace ba komai dama zancen auran mu muke da shehu, ta kalle shi koh shehu ? " yayi banza da ita ya wuce abunshi.
      Ta kalli hajiya,nagama part dina sai ki san yadda zakiyi ayi auran cikin sati daya, "hajiya ta balla mata harara, matsiya ciya ai dama nasan zuwanki ba alheri bane, " ta washe baki, karfa ki zageni kinsan nasan komai, "takaici duk ya isheta tama rasa mizata ce.

Karfe takwas na dare suka iso kano, suka wuce asibiti, " Dr aesherh dangusau ce on duty, da sauri ta tarbesu sanin tasan dazuwan su, suna zaune a office dinta ta gama duba hanifa ta kalle su, babyn ba wani serious sickness take ba, dou rashin appetite ke hana ta cin abinci, ta dau pen da paper, "ta mata prescribing paracetamol syrup na pain relieve, da Oral rehydration salt na restoring body fluid & electrolytes lost due to dehydration, idan tasha zataji dama sosai tace
     " ta mika mai paper ya karba tace baby dinnan sam bata kama da mamanta, kamar ku da ita yayi yawa, "nan gaban kursum ya buga, sai yanxu ta kara tabbatar wa da kaman yayi yawa"
    shiko yazid ko acikin shi, dan baiga kaman komai ba.
Suka fito zuwa pharmacy sukayi kicibis da umma ta shigo, "kursum tayi murmushi ta gaida ta aladabce, ta amsa da fara'arta ta amshi hanifa,
    " yazid yace umma barin barku anan inje amso magani, tace OK.
      Taja ta suka samu guri suka zauna, ta kalle kursum tace sumy kinsan na dauke ki tamkar nina haifeki, "yazid ya gayamin komai yanxu gayamin waye uban hanifa ?
     tayi narai narai da ido, aranta tace danki ne ubanta........afili tarasa mi zatace kawai ta fashe da kuka, " jikin umma yayi sanyi matuka, kar kiyi kuka kinji, am sure kina da kamun kai, saidai ko u are a victim of rape..
      "kursum tayi shuru batace komai ba illa sharar kwalla da take, "umma tace kirki damu haka Allah ya kaddara, so if u nid any1 to talk to kina iya xuwa kisame ni, kinji ?
      " toh umma nagode sosai da kulawarki, aranta tace da umma ce mahaifiyar ta da nayi sa'ar uwa." ya dawo rike da maganin, ya amshi hanifa  yace muje koh
   suka mike zasu wuce umma taja shi gefe, my son plz karka ce xaka rabu sumy, yanxu yakamta mu taimake ta, kasan yan gidansu ba sonta suke ba,
        'karki damu umma no matter wat ina tare da ita, I will 4ever luv her till eternity.
    tayi murmushi, tnx my son, tayi sallama da kursum ta wuce gida.
  shima yaja mota suka bar asibiti.

tana zaune a parlour nurse ta shigo tace hajiya lokacin shan magani yayi, "ta yatsine fuska ke nifa karki takura ni da magani, da safe ma nasha.
     nurse tace kiyi hakuri, aiki na in kula da lafiyar ki, idan baki sha ba abakin aiki na, zee dake kallon tv taja tsaki ta mike, kun cika min kunne da surutu, "hajiya tace baa dole saiki tafi daki kiyi kallo.
     "turo wan kofan ne yasata tsayawa chak, ganin su tare ga kursum rike da yarinya, ta bata rai, ku kuma da ga ina adaran nan ?
     ko kallanta basuyi ba suka karasa wajan hajiya suka gaida ta, "ta amsa ayatsine ganinsu da yar yarinya da bazata wuce 1year ba, aranta tace Allah kadai yasan ina suka samota, "tayi gyaran murya, ina jin motsin yara, yazid kazo da baby ne ??
     "kursum tayi caraf tace eh ya'ta dama ita naje dauko wa a bauchi.
Daga zee har hajiya sai da suka tsorata, lokaci guda suka ce badai shegiya bace.
      tayi banza dasu, yazid yace ba shegiya bace
     zee data gama kulewa tace kaine ubanta kenan
     "yace bani bane amma daga yau nazama ubanta.

hajiya tace zainab kiramin gimbiya in ji daga bakinta, dan bazan yadda da shegia agidan nan ba......

Dam gaban kursum ya buga, Allah yasa kar gimbiya ta kufsa mata....

            *Xarah Bukar*😘

    *Dedicated to Bady Social*

~luv u all~😘😘😘

🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺

         🌺🌺 by ~ Xarah Bêê

Page 5⃣9⃣✨

Hankali kwance ta shigo palon, ganin kursum rike da hanifa yasa tasha jinin cikinta, aranta tace oooh family drama dinsu baya karewa.
    "hajiya lafia kika naima na ?
   Ta wurga mata harara, gayamin zakiyi ya akai sumy tayi ciki harta haihu bani da labari ?
   " gimbiya ta kwashe da dariya, abu mai sauki ai ita zaki tambaya bani ba, "zee tayi caraf tace dama bakin ku daya, kun gama karuwanci ku tare ai dole ki rufa mata asiri,
   Hajiya ta daka mata tsawa, ke banson hauka anan, tunda sunki magana kawai tadau shegiar yar'ta ta maida ta inda ta dauko ta.
   "Yazid da takaici ya ishe shi yace babu inda xata , infact aurenta xanyi sai inga mai ce wa yar'mu shegia, " daga kursum har zee saida suka girgiza jin kalaman sa
    Xee ta fashe ihu, baby akan karuwa zaka gujeni, toh wlh baka isaba, ke kuma kin gama iskanci a duniya shine zaki lake mai dan matsiyaciyar yarki tasamu uba ,"kursum data gama fusata ta nunata da yatsa, kince min karuwa nayi shuru, don't u dare insult my daughter....
      "zee ta yi kwafa tace na zaga din shegia, du your worst....tass din kakkyawa marin da taji a kuncin ta yasa ta mut  lokaci daya, " ya wurga mata harara, kara  zakinta kiga abunda zan miki, marar  hankali kawai, yaja hannun kursum suka hau sama.
    Zee dake hawaye ta kalli hajiya tace ki taimaka kar ya aureta yabar ni , "hajiya taja tsaki, indai zai aureta aina ji dadi, barinta gidan nan shine farin cikina,
     gimbiya tayi shewa, buki bidiri👯 aure biyu zaai  kenan, " akule zee ta kalleta, ke kuma yar bariki wazai kwashe ki ? "tayi fari da ido, ashe baki da labari toh ubanki ne zai kwashe ni, aure nan da kwana uku, " haushi da takaici ya hana ta magana, ta suri Jakarta ta fice daga gidan.

Har dakinta ya shigo da ita,  ta kwantar da hanifa, ta kifa kai kan gado tana zubda hawaye, "yana tsaye yana kallonta, tausayi da tsananin sonta yaci gaba da ratsa shi, ya yarfe hannuwa gami da durkusawa a gabanta, " kukan nan naki na breaking heart dina, atleast say sumtim ko zanji dadi.
   "Ta dago idonta da ya sauya launi tana dubansa, ta kwantar da kai tace ya yazid I don't deserve ur love saboda ni ba wace kake tunani bace, " yayi murmushi, ai nasan u wia adopted, hajiya ba mom dinki, kar kiyi tunanin kozan ki'ke dan baki da asali, "ta kalleshi da mamaki, aranta tace nikam ba haka nake nufi ba, inason gayama wace ce ni amma ina tsoron karka gujeni, " afili ta nisa tace yaya just go I need some space, ya kalleta okay I'll but promise me u won't cry again,
     "tace yes I promise
          "ok gud nyt

" ya sauko yama hajiya sai da safe ya fice daga gidan.

gimbiya tayi murmushi mugunta, yanxu inta auri shehu tazama queen of d house, shiyasa baza ta gayawa kursum cewa yazid yayanta ne ba, gwanda ta aure shi tabar mata gidan....hmm( wa'iyazubillah gimbiya kiji tsoron Allah, dukda munsan  basu hada jiniba bai kamata kice haka ba ).

************************
Tana bacci taji an daka mata duka, firgigit ta tashi tana murtsuka ido,"miye haka zaki dakeni?
      "Meerah tace nayi mamakin ganin kine, yaushe kika zo ? Zee ta gyara kwanciya, ke nifa jiya da daddare na shigo, tension yamin yawa datx y nazo ke kuma as usual bakya nan,
    Meerah ta kwalalo ido, galfrnd wana  tension, gayamin miya Sameki, "humm ta nisa, ta fyade mata biri har wutsiya
   " meerah tace anya cousin sis dinki ba jazz tama ya yazid ba, ta gama yawon duniya harda shegia gareta but still he is willing 2 marry her, "zee tace babu wani jazz, dama yana dason yara, ni yanxu bansan ya xanyi ba, ga p.D yace mu bashi nan da sati biu, " meerah tace karki damu muna da hope ai nasan detective zai samo komai akanta, ita kuma gimbiya ki shareta naga alama matar ba mutunci.
       "aiko dai, ni bansan hw cms baba ya yadda da aurenta ba, koda yake datz his problem not mine.

Abba yayi doguwa ajiyar zuciya ya kalli umma yace narasa miyasa kike son yazid ya aure yarinyan nan alhalin kuma har ciki shege tayi, " ta bata rai, haba alhaji karka ce haka, kowa arayuwa yana da nasa laifin dan ya aureta aiba haram bane,
      "ya nisa yace toh shi kenan xanje wajan shehu naima mai auranta, amma kisani duk abunda ya faru nan gaba babu ruwana, " umma tayi murmushi, babu abunda zai faru sai alheri, yace toh nidai nagama magana, yadau hulansa ya fice.

Tun daga wannan ranar wata irin soyayya suke gudanarwa mai cike da kauna, wani lokaci abin yakan baiwa kursum mamaki, shin dama zuciya takan iya son abunda ta tsana da fari ,domin ko taki ko taso ayanxu tasan dan zaman da tayi da yazid takamu da sonshi, dan ba karamin kula da hanifa yake  ba......

Salma ce  tazo gidan, suka gaisa da samira dake rike da hanifa, "samira Ina kike samu pretty gal ?
    " tayi dariya tace ai diyar Antee sumy ce, "salma data cika da mamaki tace sumy na daki ? Tace eh tana nan.
    " ta shigo dakin, kursum dake zauna tana shafa mai tayi dariya, kawata yanxu nake shirin calling dinki, salma tayi yake, nima kasuwa zani shine nabiyo, yau baki je office ba, "eh kwana biu bana zuwa, dayake ya'ta bata jin dadi.
     Salma tace wai dagaske yar' kice , nidai ban yadda ba, sam baku kama,
" kursum ta sauke ajiyan zuciya, ta tashi ta rufe kofan dakin da mukulli, taja hannu salma suka zauna kan gado, tace kawata yau xan gayamaki sirrin rayuwata, ta tsara mata komai tun daga ranar da mahaifiyar ta tayar da ita har izuwa yau, "ba karamin tausaya mata tai ba tace Allah yaji kan sumy, ni aganina it better ki gayawa yazid gaskia yasan cewa shine uban hanifa,
     " kursum ta nisa, inason gayamai ina tsoro karya gujeni, "salma tace karki ji tsoro, ba karamin sonki yake ba am sure he will understand idan kika gayamai, tace toh I will try idan nasamu chance, " wana  chance kuma kike naima inji salma, kinsan already kinyi committing babban crime by impersonating a dead person , wlh d earlier d better, ki gayamai da wuri tun kafin yaji abakin wasu,
   "Jikin kursum yay sanyi ba kadan ba, dole ta gayamai yau idan yazo," kawata nagode sosai da shawaranki, salma tayi murmushi, Allah yasa adace kawai, nizan wuce yanxu, kidai tabbata kin gayamai, kursum tace toh, ta mike ta raka salma har bakin gate, salma tace wai make faruwa ne, dazu naga wasu mata da niki nikin akwatuna sun shigo,
    "Haba dai nikam banga kowa ba inji kursum
   Salma tace OK sai dai munyi waya, sukayi sallama ta wuce.

Samira!! samira!! " da sauri ta fito daga kitchen, gani Antee sumy, kursum tace ina hanifa ? , tayi bacci nakaita daki....
         "wasu mata ne sukazo dazu bansani ba?
      samira tace yan'uwan gimbiya, biki suka zo , suna bangaran baki
       kursum ta kwalalo ido waje, wa xaiyi aure a gidan nan ? ,"Antee baki da labarin baba shehu zai auri gimbiya gobe...
    " kasa magana tayi dan takaici, afusace ta wuce dakin gimbiya
   Gimbiya na baje adaki sai lissafi kayan dazata siyo take, kursum ta bango kofa ta shigo, tafara wurgi da kayan gimbiya, yau dole kibar gidan nan, gimbiya tace kursum miye haka ?
     "Ta wurga mata harara, ban taba sanin ke makira CE ba sai yanxu, ashe ke kika tura acewa ex mijin sumy tayi aure tabar gari, toh yau karya ki takare dan nima yanxu xan fasa kwai, ke kibar gidan nikuma dama nasamu mijin aure.
     "Gimbiya tayi tsuru tsuru tabbas dagaske kursum take ba alama wasa, tana iya wurga ta waje, ta nisa tace kursum kiyi min hakuri nasan nayi laifi, ki bari idan na auri  Shehu saiki tona asiri.
        Kursum data gama kulewa tace baki isa ba, u must leave yanxu nan, ta shiga tura akwatu nan ta waje, " gimbiya dukta gigice tarasa abun cewa, can dabara ta fado mata, tace kursum naga mahaifiyar ki.......
      
"Chak ta tsaya, karya kike, so kike ki raina min hankali
    
       gimbiya tace wlh dagaske nake, ta zazzage kayan ta, ta dauko wani karamin pink hankie da takarda aciki ta mika mata
    Kursum ta amsa, na miye wannan?
       " tace mahaifiyar ki taban ranar data kawoki wajena,
      "da sauri ta bude, ba wasu rubutu masu yawa bane, " kursum aka rubuta daga sama, daga kasa akasa lovely Mom......
        Agigice ta kalleta, wace ce mahaifiya ta?
   
    "gimbiya tace ba kowa bace face umma dake zuwa gidan nan......
      Dammm, lokaci guda zufa yafara keto mata, umma !! umma!! ta kira yafi a dirga, Umma y did u abandon me, u'r such a nice woman, " kuka kawai take hankali tashe, sai yanxu ta tabbatar shakuwar su da umma ba abanza bane.........

              *Xarah Bukar*😘

*Dedicated to Bady social*

~luv u all~😘😘😘

[16/09 10:09 pm] Xarah bukar✍🏻✍🏻:
🌺🌺🌺 KURSUM 🌺🌺

         🌺🌺 by ~Xarah Bêê

Page 6⃣0⃣✨

Ta dago idonta daya sauya launi tsabar kuka, ta kalleta tace kin cuceni,  kinsan umma ce mahaifiyata shine kika boyemin har nayi falling in luv da yayana na jini bansani ba, Y ?, miyasa kike min haka ??
     "Gimbiya tayi wiki wiki da ido, kiyi hakuri, mantawa nayi ban gayamaki ba, tunda yanxu kin kasani ba kuka zakiyi ba, tattarawa zakiyi ki koma gidan ta.....
    Haushi da takaicin kalamata ya hana kursum ce mata uffan, afusace ta fice takoma dakin ta ....

Baba shehu ne tare da abba suna xantawa, "abba yayi dariya yace nazo nai mawa da'na aure ashe kaima auran xakayi....." Yayi yake yace kasan aure lokaci ne, idan yazo dole ayi, ashe ya'yan namu sun shirya sai aure kenan, "Abba ya murmusa, shine dai ya nace yana sonta ,kasan yaran zamani sai abunda suke so
       " baba shehu yace ai gwara ayi auran nan da sati biyu zaifi, dan nagaji daganin zainab ba aure, "abba ya numfasa, ba zainan nake nufi ba, yar wajan hadiza data dawo kwanaki nake nufi, " dif annurin fuskan baba shehu ya dauke, aranshi yana mamakin karfi halin irin na alhaji Imam, wato karuwa ya zaba akan yar'sa.....
     Ya kirkiro murmushi dole yace xainab da sumayya duk ya'yana ne, karma ka wahalar dakan ka, na bawa danka ita har abada, idan kun shirya ana iya auran asati biyu kacal....
   "ba karamin dadi Abba yaji ba, burinsa bai wuce yaga yazid yay aure, yama baba shehu godiya sosai Burinsa yaga yazid yay aure, suka tsaida rana nan da sati biyu kacal, sunyi hira sosai, daga bisani daddy yamai godiya ya fice.
  
  Baba shehu kaman ya fasa ihu dan haushi, da sauri yay dialling no din p.D....
          "hello detective ya ake ciki ne ?
    p.D yace Alhaji munata bincike dai, nan da sati daya zan kawo report din komai...
     " okay, ka gaggauta cox we are running out of tym, p.D yace ba matsala munsa kan aikimu.

Har dare tana zaune a daki ba mafita, taci kuka harta gaji daga bisani ta tashi ta dauro alwala tahau salloli.

Washe gari aka daure aure baba shehu da gimbiya, babu wanda ke farin cikin aure, "sai shewa suke a parlour suna dariya, Hinde kawarta tace wai ina masu gidan ne ?? naga tunda mukazo babu wanda ya tarbe mu
      " gimbiya taja tsaki, aini ba ruwana dasu tunda nazama matar gidan, ina samun dukiyar su xan gudu bazasu kara gani na ba....hinde ta kwashe da dariya, gaskia kawata kinyi dabara , ko gidan nan kika samu  kin more ba kadan ba, nidai kima mijin naki magana yay employing dina a company dinsu, "gimbiya ta balla mata harara tace keda kike nurse a psychiatric hospital miye na kwalaman     aiki da mijina, indai aiki kikeso xan baki,
     Wana aiki zaki ban ?
"ta murmusa tace aiki ne mai sauki , kinga nurse din hajiya ta tafi jiya, so xaki zama in charge of kula da lafiyan ta da bata magani
    Hinde ta bata rai, shi maganin bata iya sha sai an bata.....gimbiya tace ke wawiya ce wlh, maganin dazai gusar mata da kwakwalwa nakeso ki bata, kinga  idan dosage yamata yawa zata fara hauka saimu kaita psychiatric,  shine kadai zaiza insamu dukiyar gidan nan hankali kwance😊
       " kin samu dukiyar ni kuma fah ? inji hinde,
          "haba kawas idan nasamu 50-50 xamuyi mana
       Hmmm kawai hinde tayi, tasan halin hafsatu da kudi, amma zatai aikin.

Shiga na alfarma tayi ta fito rike da hanifa, ta leke dakin hajiya, chan ta hangota kwance kan gado tana bacci, karasa wa ciki tayi ahankali, ta kare mata kallo, aranta tace Allah kadai yasan maike damun hajiya, ta lura she is alwyz depress, ta janyo blanket ta  rufeta sannan ta fita

Tana sauko wa suka bita da ido, ko kallan su batai ba tayi waje, hinde tace itace kursum ? "gimbiya ta yatsine fuska, itace fah, amma banda case da ita already matsalolin rayuwa sun mata yawa.

Yana zaune cikin mota, ta bude ta shiga, ta kalleshi tai murmushi, sorry 4 keeping u wait
        "ya lumshe sexy eyes dinshi yaja mota ,yace am not complaining, ya taba cheeks din hanifa, cutie bakya magana sai murmushi alwyz, " kursum tace datz wat u have in common, kasan jini baya karya
         "yace I don't understand, jinin wa kuma ?
       Da sauri ta share xancen tace I cnt wait 2 c umma, kwana biyu nayi missing dinta, plz ya yazid mu tsaya shoprite ensai mata sumtin special
     " yay murmushi, toh yar umma, ni kuma mi zaki siyamin ?
       "caraf tace nothing, amma xan siyawa sister dinka chocolate...
        " banda sister ai, ni kadai umma ta haifa a duniya, so dat chocolate belongs 2 me...
     "Jikinta yay sanyi, dama da gangan tamai batun sister dan taji mai xaice, she has to b sure ko dagaske umma ce mahaifiyar ta

Sun iso shoprite, ya kalleta da alama tayi zurfi cikin tunani, ya tabo ta, " hey are u alright ?
       "firgigit ta dawo hayyacinta, hmm yea am okay
       " yace muje koh
  tace toh...
 
Siyayya na gani na fada tama umma, ita kanta batasan iya adadin turaruka da super wax din data kwasa ba, taje counter akamata package din komai, ta mika credit card dinta, daya daga cikin agent yace madam ur bill is settled
         "Okay kawai tace tasan shine ya biya, yana tsaye awaje tare da hanifa......

Hankali kwance ta fito, bata Ankara ba taji an bangaje ta, tana dagowa sukai 4 eyes da zee tare da meerah, " zee ta kalle meerah, galfrnd ga karuwar data min snatching ya yazid, meerah data shagala da kallon kursum tace not bad, she is pretty, so I don't blame him..
      "Rai abace kursum ta balla masu harara, tace zee banda lokaci, bad behaviour dinnan naki yasa ya yazid yayi dumping dinki a dustbin,
      " zee tai kwafa tace cousin sis ur dayx are numbered, tsakani na dake zamuga waye bad person, kuma ki rubuta ki ajiye nice matar ya yazid bake ba..
      "hmm kawai kursum tace, ta raba ta gefe tawuce...
     " meerah tace galfrnd dole ki susuce, ur sis is damm pretty, I tot ko irin village gals dinnan nan
     tsaki zee tayi, kizo mu fara shopping kar dare yayi, ko kema kin kamu ne ?
       "Aaah haba dai, kinsan kece tawa

Koda ta dawo bata nuna mai ta hadu da zee ba, sai murmushin dole data kirkiro, yaja mota har gidan umma.....

Umma na zaune a parlour suka shigo, ba karamin dadi taji ba, dan batasan da zuwan su ba, "har kasa kursum ta duka suna gaisa, ta amshi hanifa dake bacci tace yaudai sumy tazo gidan ummata, " kursum sai sunne kai take, gabadaya she is not comfortable saboda wani irin  mayataccan kallo da ya yazid ke mata, "umma dake lura dasu ta kalli ya yazid tace my son na bar glasses dina a mota jeka dauko min, sum sum ya tashi, umma tai murmushi, daughter sannu da kokari duk kayan nan nawa ne
      " kursum tai shuru, ita dai abunda ya kawota gidan bai wuce tasan ko umma ce uwarta ba,
    Umma tace ga hanifa kaita dakina ta kwanta, barin duba masu aiki a kitchen
      "tace toh, ta amshe ta..
 
Tana shiga dakin ta ajiye hanifa kan gado, ta zuge jarkar ta dauko dan karamin paper da gimbiya taba ta, ta kalli rubutun, aranta tace dole ta binciko any note mai rubutun umma dan tayi comparing ko ita ta rubuta....

Da sauri tahau bincike, taja side drawer taga magazines dayawa, ta fiddo su gabadaya tana dubawa, dakyar tasamu karamin memo mai rubutu aciki, tayi comparing, sam baizo daya ba, nan take tafara zubda hawaye
      " bata Ankara ba saiji tayi umma tace lafiya kikemin bincike ?
     Agigice ta juyo ta kalleta, tace umma plz ki gayamin gaskia ke kika haifeni ?
       umma ta kwalalo ido, bangane mai kike nufi ba ?
  "Kursum ta mika mata karamin paper din, tace kin tuna wannan ?
      Umma ta karba ta duba, ta kalli kursum a tsorace tace ina kika samu paper dinnan ? wace CE ke???

             *Xarah Bukar*😘
*Dedicated to Bady social*

~Luv u all~😘😘😘

No comments:

Post a Comment